Ganduje Ya Bukaci Abba Gida-Gida Ya Ƙarasa Wasu Ayyuka a Kano

Ganduje Ya Bukaci Abba Gida-Gida Ya Ƙarasa Wasu Ayyuka a Kano

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya roki Abba Kabir Yusuf ya taimaka ya karissa ayyukan da ya fara
  • A wata sanarwan barka da Sallah da kwamsihinan yaɗa labarai ya fitar, Ganduje ya ce ya yafe wa kowa
  • Ya kuma gode wa Allah bisa shafe shekaru 20 yana ba da gudummuwa a gwamnatance

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce bai riƙi kowa a cikin zuciyarsa ba tun farkon mulkinsa wanda zai ƙare ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Gwamna Ganduje na jam'iyyar APC ya roƙi magajinsa, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya ƙarisa ayyukan da gwamnatinsa ta fara amma ba ta sami damar ƙarisa wa ba.

Abba da Ganduje.
Ganduje Ya Bukaci Abba Gida-Gida Ya Karisa Wasu Ayyuka a Kano Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels tv ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a sakon Barka da Sallah wanda kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya fitar ranar Jummu'a.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Gabatar Da Wata Muhimmiyar Bukata 1 Tak Da Yake So Abba Gida-Gida Ya Cika Masa

A sanarwan, gwamna Ganduje ya kara gode wa Allah mai girma da ɗaukaka bisa damar da ya ba shi na ba da gudummuwa a harkar shugabanci tsawon shekaru 20.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan Kano ya ce:

"Ina da manyan dalilan da zan ƙara gode wa Allah, ban taɓa jin haushi ko na riƙe wani a zuciyata ba, na yafe wa duk wanda ya mun ba daidai ba, ina fatan ku ma zaku yafe mun."

Haka nan Ganduje ya yi kira ga ɗaukacin mabiya addinin Musulunci su ɗauki darussan watan Ramadan, wanda ya koyar mana ƙaunar juna da taimakon juna.

Ya kuma roki Musulmai suci gaba da addu'ar neman zaman lafiya da ci gaba a jihar Kano da kuma ƙasa baki ɗaya, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Ganduje ya roki Abba Gida-Gida

Kara karanta wannan

A Masallacin Idi, Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Atiku da Wasu Mutane a Najeriya

Bayan nan Gwamna Ganduje ya yi bayanin amfanin ci gaba da ayyuka na gari kuma ya roki gwamnati mai zuwa karkashin Abba Kabir Yusuf, ta ƙarisa ayyukan da gwamnati mai ci ta faro.

"Muna kira ga gwamnati mai jiran gado ta tabbata ta ƙarisa ayyukan da lokaci ya hana wannan gwamnatin kammala wa domin amfanin talakawan jihar."

A wani labarin kuma Matashin Da Ya Ci Zaben Dan Majalisar Tarayya a Jihar Taraba Ya Rasu

Allah ya yi wa zababɓen ɗan majalisar tarayya dan shekara 36 rasuwa yau Asabar.

Ismaila Maihanci ya ci zaɓen ɗan majalisar wakilan tarayya a inuwar PDP. Bayanai sun nuna anjima za'a masa Jana'iza kamar yadda Musulunci ya tanada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel