Eid-El-Fitr: Ku Rungumi Hukuncin Kotun Zabe Da Imani, Sultan Ga Marasa Nasara

Eid-El-Fitr: Ku Rungumi Hukuncin Kotun Zabe Da Imani, Sultan Ga Marasa Nasara

  • Sultan na Sakkwato ya roki dukkan yan takarar da Allah bai ba mulki ba su yi hakuri su rungumi duk abinda Kotu ta yanke
  • Alhaji Sa'ad Abubakar III ya yi wannan furucin ne a cikin sakonsa na barka da Sallah jim kaɗan bayan kammala Sallar idi a Sakkwato
  • Sarkin Musulmai ya ƙara gode wa Allah bisa ni'imar raya mutane suka ga ƙaramar Sallah ta bana

Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya roƙi 'yan takara, waɗanda suka nufi Kotu bayan sun sha kaye a babban zaɓen 2023, su rungumi duk hukuncin da Kotu ta yanke.

Sultan na Sakkwato ya yi wannan magana ne a sakon barka da Sallah jim kaɗan bayan kammala Sallar Eid-El-Fitr a Fakon idi, filin hawa idi ranar Jumu'a, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Atiku Ya Fadi Abin da Yake Damunsa, Tinubu Ya Yi kira ga Musulmi

Sarkin Musulmai.
Eid-El-Fitr: Ku Rungumi Hukuncin Kotun Zabe Da Imani, Sultan Ga Marasa Nasara Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Sultan ya ce matakin da Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran yan takarar da suka sha kaye a zaɓe a dukkan matakai suka ɗauka na zuwa Kotun doka maimakon ta da zaune tsaye abun a yaba ne.

Abubakar ya kuma roki duk ɗan takarar da ya kai ƙara Ƙotu ya shirya karban duk hukuncin da Alƙali ya yanke ko da kuwa bai zo musu da daɗi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bayan aminta da sakamakon, ku mara wa waɗanda suka samu nasara baya domin samun dawwamammen zaman lafiya, haɗin kai da kuma ci gaba," inji Sultan.

Sarkin Musulmin ya kuma ƙara gode wa Allah SWT, "Wanda ya raya mu har muka shaida ranar sallar idi ƙarama," bayan kammala Azumin watan Ramadan.

Ya ce:

"A matsayin mutane bayin Allah, ya zama wajibi mu ƙara gode wa Allah SWT bisa ni'imar da ya mana ta rayuwa da ƙoshin lafiya, da kuma kasancewa cikin waɗanda zasu yi murnar zuwan wannan rana mai Albarka."

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wasu Muggan Mutane Sama da 20 Ɗauke da Makamai Ana Dab da Sallah a Arewa

"Mun koyi abubuwa da dama daga wurin Malamanmu a lokacin azumin watan Ramadan. Ya kamata mu yi amfani da duk abinda muka koya a rayuwar yau da kullum."

Abubuwa 7 game da karamar Sallah

A wani labarin kuma Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game da Karamar Sallah a Musulunci

A ranar Jummu'a 21 ga watan Afrilu, 2023, al'ummar Musulmai suka gudanar da Sallar idin ƙaramar Sallah a Najeriya da wasu ƙasashe.

Mun zakulo muku wasu muhimman abubuwa masu girma game da Eid-El-Fitr bayan gama Azumin watan Ramadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel