Zababben Gwamna Ya Karbi Satifiket Din Lashe Zabe, Ya Sha Wani Babban Alwashi

Zababben Gwamna Ya Karbi Satifiket Din Lashe Zabe, Ya Sha Wani Babban Alwashi

  • Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kebbi ya samu amsar satifiket ɗin lashe zaɓen gwamnan jihar a hannun INEC
  • Dr Nasiru Idris ya kuma sha alwashin ɗorawa daga inda gwamna mai barin gado na jihar ya tsaya
  • Zaɓaɓɓen gwamnan ya kuma yi alƙawarin cewa zai tabbatar da cewa ya cika alƙawuran da ya ɗauka ga mutanen jihar

Jihar Kebbi - Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasiru Idris, ya karɓi satifiket ɗin lashe zaɓen gwamnan jihar da ya yi, inda yayi alƙawarin kammala dukkanin ayyukan da gwamna Abubakar Bagudu bai ƙarasa ba.

Ya kuma yi alƙawarin tabbatar da cewa babban birnin jihar, Birnin Kebbi, an tada komaɗar sa ya koma na zamani, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Zababben gwamnan Kebbi ya karɓi satifiket
Zababben gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasiru Idris Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Idris ya sha wannan alwashin ne a lokacin da shi da mataimakin sa, Abubakar Tafida, suke karɓar satifiket ɗin lashe zaɓe a hedikwatar hukumar zaɓw mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta jihar da ke a Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Sanar Da Lokacin Ba Fintiri Satifiket Din Lashe Zaben Gwamna

Ya bayyana cewa a shirye yake ya dawo da martabar tattalin arziƙin jihar sannan ya tabbatar da cewa manoman yankin Kudancin jihar mai fama da rigima sun koma gonakin su bayan an rantsar da shi, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaɓaɓɓen gwamnan ya ce al'ummar jihar Kebbi, sun cancanci yin rayuwa mai inganci saboda suna da aiki tuƙuru da jajircewa wajen ganin cigaban jihar.

A kalamansa:

"Yau babbar rana ce a gare ni saboda jihar Kebbi ta kafa tarihi. Ina son na godewa al'ummar jihar bisa yarda da ni da jam'iyyar mu ta APC, na yi alƙawarin cewa nauyin da aka ɗora min ba zan yi wasa da shi ba kuma zan cika dukkanin alƙawuran da na ɗauka."

Zaɓaɓɓen gwamnan ya kuma nuna godiyar sa ga hukumar INEC da jami'an tsaro kan yadda zaɓen ya gudana cikin lumana a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan Lallasa Dan Majalisa Mai Ci a Zabe, Matashin Dan Majalisa Ya Bayyana Inda Ya Samo Kudin Kamfe

PDP Ta Garzaya Kotu Bayan APC Ta Ci Gwamna da Kuri’u 40, 000

A wani labarin na daban kuma, kun ji yadda jam'iyyar PDP a jihar Kebbi ta garzaya kotu domin ƙalubalantar zaɓen gwamnan jihar, wanda ta yi rashin nasara a hannun jam'iyyar APC.

Jam'iyyar APC ta ba PDP rata a zaɓen wacce ta kai ta ƙuri'u 40,000

Asali: Legit.ng

Online view pixel