Bayan Lallasa Dan Majalisa Mai Ci a Zabe, Matashin Dan Majalisa Ya Bayyana Inda Ya Samo Kudin Kamfe

Bayan Lallasa Dan Majalisa Mai Ci a Zabe, Matashin Dan Majalisa Ya Bayyana Inda Ya Samo Kudin Kamfe

  • Dan shekara 33 a duniya da ya doke dan majalisa mai ci daga kan kujerar sa a Sokoto ya bayyana inda ya samo kuɗin kamfe
  • Hon. Bashir Usman Gorau, ya ce ɗan noman da yake taɓa wa da kasuwanci suka samar masa da kuɗin
  • Gorau ya lashe kujerar ɗan majalisr wakilai ta tarayya bayan ya tiƙa ɗan majalisar da kwashe shekaru a kujerar

Jihar Sokoto - Matashi mai shekara 33 a duniya, Bashir Usman Gorau, wanda ya lashe zaɓen ɗan majalisar wakilai ta tarayya na mazaɓar Gada-Goronyo, ya bayyana inda ya samu kuɗin kamfen ɗin sa.

Jaridar Daily Trust tace Bashir ya bayyana cewa ya samu kuɗin kamfen ɗin sa ne ta hanyar kuɗin da yake samu a noman da yake taɓawa.

Da noma na samo kudin kamfe, Bashir Gorau
Matashin dan majalisa daga Sokoto, Bashir Usman Gorau Hoto: Comr Bashir Usman Gorau
Asali: Facebook

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da Gorau a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu ƙuri'u 29,679, inda ya hana tazarce karo na biyar na Musa Adar na jam'iyyar APC, wanda ya 25,549, cewar rahoton The Cable

Kara karanta wannan

Cikon Zaben 2023: Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Ruɗanin Zaben Gwamnan Adamawa

A wata tattaunawa da gidan talbijin na Trust tv a shirin su na 'Daily Politics' ranar Talata, Gorau ya yi bayanin cewa da shi da maigidan sa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ba su taɓa amfani da kuɗin asusun jihar ba wajen yaƙin neman zaɓen su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Ba zaka iya gayawa Tambuwal ya yi amfani da kuɗin jihar nan domin zaɓe ba, zai gaya maka idan aka je lahira kai ne zaka amsa masa tambayoyin sa ko kiwa shine zai amsa tambayoyin sa? Ina da tabbacin haka."
"Kamar ni, na samu kuɗin kamfen ɗi na ne ta hanyar noma da kasuwancin da na ke yi. Kowa ya san cewa ni manomi ne, tambayi duk wanda za ka tambaya, a tsawon wata 14 da na yi bana riƙe da ofis."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Sanar Da Lokacin Ba Fintiri Satifiket Din Lashe Zaben Gwamna

Gorau tsohon kwamishinan ci gaban matasa da wasanni ne na jihar Sokoto, ya yi takara a ƙarƙashin inuwar Peoples Democratic Party (PDP).

Nasarar da ya samu ta ƙara yawan matasan da suka lashe kujerun ƴan majalisa a babban zaɓen 2023.

Jam'iyyar APC Ta Kori Babban Sanata a Jihar Gombe

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda jam'iyyar APC ta kori babban sanatan ta mai ci a jihar Gombe dake Arewacin Najeriya.

Jam'iyysr ta kori Sanata Danjuma Goje ne, bayan samun sa da tarin laifuka..

Asali: Legit.ng

Online view pixel