Kogi 2023: Melaye Da Wasu Yan PDP 4 Da Ke Hararar Kujerar Gwamna Yahaya Bello

Kogi 2023: Melaye Da Wasu Yan PDP 4 Da Ke Hararar Kujerar Gwamna Yahaya Bello

A ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta sake samun wani dama na karbe kujerar gwamna a jihar Kogi daga hannun jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Tuni jam'iyyar PDP mai adawa ta tantance yan takara tara wadanda za su fafata a zaben fidda gwanin jam'iyyar don mallakar tikitin mai muhimmanci.

Masu neman takarar gwamnan Kogi a PDP
Kogi 2023: Melaye Da Wasu Yan PDP 4 Da Ke Hararar Kujerar Gwamna Yahaya Bello Hoto: Dino Melaye, Wada Samuel, M Sani
Asali: Facebook

Daga cikin masu neman takarar, sunayen wasu mutane biyar sun yi zarra. Ga dan takaitaccen bayanai game da manyan masu neman takarar biyar wadanda cikinsu wani ka iya mallakar tikitin PDP a zaben gwamnan Kogi.

Sanata Dino Melaye

Tsohon sanata mai wakiltan Kogi ta yamma, yana daya daga cikin jiga-jigan PDP da ke son su gaje Yahaya Bello, babban abokin hamayyarsa a siyasa, a matsayin gwamnan jihar Kogi.

Kara karanta wannan

"PDP Ba Za Ta Kai Labari Ba Idan Har Ta Ba Dino Melaye Tikitinta a Zaben Gwamnan Kogi", Wike

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana ta rade-radin cewa akwai shirye-shirye da ake yi na magudi a tsarin zaben don tabbatar da ganin cewa Melaye ne ya mallaki tikitin PDP.

Injiniya Musa Wada

Injiniya Musa Wada ba bako bane idan ana maganar siyasar jihar Kogi. Ya yi takarar gwamna a zaben 2019 a karkashin PDP amma ya sha kaye a hannun Gwamna Bello.

Tsohon dan takarar gwamnan zai yi duba da gogewarsa wajen lallasa sauran yan takarar da kuma sake mallakar tikitin PDP.

Yomi Awoniyi

Yomi Awoniyi ma fitaccen dan siyasa ne a Kogi, kasancewar ya rike mukamin mataimakin gwamnan jihar.

Tsohon mataimakin gwamnan ya kuma yi aiki a matsayin Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa a jihar Kogi, a zaben shugaban kasa na 2023.

Sanata Atai Aidoko

Sanata Atai Aidoko ya taba wakiltan yankin Kogi ta gabas a majalisar dattawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Bayan Dogon Lokaci, Gaskiyar Abinda Ya Sa Atiku Ya Sha Kaye a Zaben 2023 Ya Fito

An tsige Aidoko a 2018 kasancewar kotu ta yi watsi da shawarar PDP na gabatar da shi a matsayin dan takararta na sanata a zaben 2015, duk da ya san cewa abokin hamayyarsa Isaac Alfa ne ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar sannan INEC ta ba shi takardar shaidar cin zabe.

Abdullahi Haruna SAN

Abdullahi Haruna (SAN) wanda ya kasance babban lauya ya san ta kan siyasar jihar Kogi sosai.

Ya taba aiki a matsayin kwamishinan shari'a a jihar.

A wani labari na daban, wani malamin addini Theophilus Olabayo, ya yi ikirarin cewa babu gudu babu ja da baya za a rantsar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel