Rikici Ya Tsananta: APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya da Babban Jigo Kan Abu 1

Rikici Ya Tsananta: APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya da Babban Jigo Kan Abu 1

  • Jam'iyyar APC a jihar Ribas ta ɗauki mataki mai tsauri kan shugabanta na jiha da mai ba da shawara kan harkokin shari'a
  • Bayan haka APC ta nesanta kanta da wasu kalamai da aka ji tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, na yi kan Bola Tinubu
  • Ta miƙa shugabannin biyu ga kwamitimn bincike domin tabbatar da zargin da ake musu gaskiya ne ko akasin haka

Rivers - Kwamitin zartaswa na jam'iyyar APC reshen jihar Ribas (SEC), ranar Laraba, ya dakatar da shugbaan jam'iyya na jiha, Chief Emeka Beke, da mai ba da shawara kan shari'a, Iheanyichukwu Azubuike.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Kwamitin ya ɗauki matakin dakatar da manyan ƙusoshin guda biyu ne bisa zarginsu da cin amana da yi wa APC zagon ƙasa.

Tutar APC.
Rikici Ya Tsananta: APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya da Babban Jigo Kan Abu 1 Hoto: OfficialAPCNg
Asali: Instagram

Haka zalika SEC ya nesanta kansa da kalaman tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya yi ikirarin cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ne ya naɗa shugaban INEC.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan PDP, Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa da Wasu Shugabanni 3

Shugaban kwamitin SEC-APC, Chike Eyinda, ne ya bayyana haka yayin da ya jagoranci sauran mambobin kwamitin zuwa wurin hira da 'yan jarida ranar Laraba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Eyinda ya bayyana cewa ayyukan Amaechi da Beke sun taka rawa wajen durkusad da jam'iyyar, kuma su ne suka jawo jam'iyyar ta sha kashi a babban zaɓen 2023 da aka gama a Ribas.

A rahoton Vanguard, A jawabinsa ya ce:

"Mu mambobin kwamitin zartaswa na jiha mun cimma matsayar dakatar da shugaban jam'iyya, Chef Emeka Beke, har sai baba ta gani bisa zargin cin amana, sulalewar kudi har sai an gama bincike."
"Daga nan zuwa lokacin da kwamiti zai kammala rahotom bincike, mataimakinsa, Mr. Omiete Eferebo, zai maye gurbin a matsayin shugaban jam'iyya na riko nan take."
"Haka nan mun amince da dakatar da mashawarci kan harkokin shari'a, Iheanyichukwu Azubuike, bisa zargin cin amana da batan kuɗi har sai lokacin da aka gama bincike."

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 da Suka Auka Matsalar Zabe Bayan Yin Fito Na Fito da Buhari a Kan Canjin Kudi

Matasan Jam'iyyar APC Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Ondo

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Kama Hanyar Rugujewa, Wasu Shugabanni da Matasa Sun Kara Kawo Cikas

Yayin da PDP ke kokarin farfaɗowa daga rigingimun da take ciki, wasu gungun matasa sun maida hannun agogo baya a jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262