Yan Sanda Sun Bayyana Yan Daban Siyasa 17 Da Ake Zargi a Nasarawa

Yan Sanda Sun Bayyana Yan Daban Siyasa 17 Da Ake Zargi a Nasarawa

  • Hukumar yan sanda ta bayyana fuskokin mutane 17 da ake zargin yan daba ne a jihar Nasarawa
  • Mai magana da yawun hukumar, DSP Nansel, ya ce mutanen sun shiga hannu ne a lokacin babban zaɓe
  • Ya bayyana sunayensu baki ɗaya kana ya ce da zaran sun gama bincike zasu maka waɗanda ake zargin a gaban kuliya

Nasarawa - Hukumar 'yan sanda a jihar Nasarawa ta nuna jerin mutane 17 da ake zargin 'yan daban siyasa ne da suka aikata laifuka daban-daban a zaɓen da aka kammala.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sanda reshen jihar, Ramhan Nansel, ne ya bayyana fuskokin 'yan daban a Shelkwatar 'yan sanda da ke Lafiya, ranar Lahadi.

Yan daban siyasa.
Yan Sanda Sun Bayyana Yan Daban Siyasa 17 Da Ake Zargi a Nasarawa Hoto: PoliceNG
Asali: UGC

Ya ce jami'an tsaro sun kama waɗanda ake zargin ɗauke da bingidu da harsasai, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin daga jihar Imo aka ɗauko hayarsu, wasu kuma Abuja da ke maƙota da jihar da nufin kawo cikas yayin zaɓe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, tun da fari kwamishinan 'yan sanda, Maiyaki Muhammed Baba, ya ankarar da cewa da yuwuwar wasu 'yan siyasa su shigo da baƙin 'yan daba domin ta da yamutsi a zaben shugaban kasa.

DSP Nansel, yace duk da gargaɗin da hukumar ta yi, sai da wasu gurbatattu suka yi yunkurin shigowa jihar ta bakin boda.

Yace Sojoji suka damke motocin Toyota pickup da Toyota Siena SUV maƙare da 'yan daba a Umaisha, ƙaramar hukumar Toto, ana dab da zaben 18 ga watan Maris, 2023.

"Yayin bincike an gano suna ɗauke da bindigu manya biyu, bindigu kirar cikin gida 9, ƙunshin harsasai 20, Wayoyin kamfanoni daban-daban 24, motoci biyu marasa lamba, rigar sulke da sauransu," inji Nansel.

Jerin sunayen mutanen da aka kama

Kakakin yan sandan ya bayyana sunayen 'yan daban wanda suka haɗa da, Aaron Samson, Tijani Jemba, Abdulahi Salihu, Usman Abubakar, Abdulahi Usman, da Mohammed Abdulahi.

Sauran sun ƙunshi Babangida Mohammed, Kasimu A. Danladi, Saidu A. Suleiman, Salihu Abdulkareem, Shamsudeen Abubakar, Usman Murtala, Mohammed Sule, Huseini Elhag, James Emeka, Idris Abdullazeez da Ibrahim Alhassan.

Yace da zaran jami'ai sun kammala bincike za'a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban Kotu domin su girbi abinda suka shuka, kamar yadda The Cable ta rahoto.

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya Sun Halaka Babban Ɗan Ta'adda da Wasu Mayaƙa Sama da 40 a Arewa

Wata majiya daga jami'an soji ta bayyana cewa Sojojin da haɗin kan dakarun CJTF sun sheƙe yan ta'addan a yankin Dikwa a Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel