2023: An Tsinci Gawar Ɗan Takarar Gwamnan Imo Na Jam'iyyar LP

2023: An Tsinci Gawar Ɗan Takarar Gwamnan Imo Na Jam'iyyar LP

  • Allah ya yi wa ɗan takarar gwamnan jihar Imo a inuwar LP, Humphrey Anumudu, rasuwa jim kaɗan bayan ya dawo daga Abuja
  • Bayanai sun nuna an gano gawar ɗan siyasan a gidansa da ke jihar Legas bayan ya halarci wani taron LP
  • Tun 1998 yake neman zama gwamnan Imo kuma a wannan karon ma ya shiga zaben fidda gwanin Labour Party

Lagos - Rahotanni sun nuna cewa an tsinci gawar ɗan takarar da ke neman tikitin takarar gwamna a inuwar Labour Party a zaben fidda gwanin da ke tafe a jihar Imo, Chief Humphrey Anumudu.

Tribune Online ta rahoto cewa ɗan takarar ya mutu ne a gidansa da ke jihar Legas, bayan ya dawo daga taron LP wanda ya gudana a Hedkwatar jam'iyya ta ƙasa da ke Abuja ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara

Dan takarar LP, Humphrey Anumudu.
Marigayi Humphrey Anumudu Hoto: tribune
Asali: UGC

Jihar Imo na ɗaya daga cikin jihohin da INEC ke gudanar da zaben gwamna a lokaci daban da babban zaɓe kuma a yanzu, jam'iyyu sun fara shirin tsaida yan takara.

Me ya yi ajalin ɗan siyasan?

Jigon siyasan, haifaffen yankin masarautar Mbieri, ƙaramar hukumar Mbaitoli a jihar Imo, Anumudu, bayanai sun nuna an tsinci gawarsa a gida a yanayin da iyalansa suka kira da, "Farmakin ruhi."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A matsayinsa na Biliyoniyan ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa, ya jima yana neman takarar zama gwamnan jihar Imo da ke arewa maso gabashin Najeriya, tun 1998.

An ce shi ne halastaccen wanda ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a shekarar 1998 kafin daga bisani a miƙa wa Achike Udenwa, wanda ya mulki Imo daga 1999 zuwa 2007.

Tun wancan lokacin yake neman zama kujera lamba ɗaya a jihar. A zaɓen 2019, shi ne ɗan takarar gwamna karkashin inuwar Zenith Labour party.

Kara karanta wannan

Yan Jagaliya Sun Kaddamar da Hari a Ofishin APC dake Zamfara, Biyu Sun Tafi Lahira

Wani abokin mamacin na kusa-kusa ya ce ɗan siyasan ya mutu ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Jummu'a 24 ga watan Maris, 2023, kamar yadda Punch ta rahoto.

Bayanai sun nuna cewa mamacin ya riga ya biya miliyan N25m kuɗin Fam ɗin tsayawa takarar gwamna na jam'iyyar LP a zaben Imo da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Coci, Sun sace Matarsa a jihar Kaduna

Shugaban CAN reshen jihar, Rabaran Hayab, ya ce bayan halaka malamin, yan ta'adda sun sako sama da mutum 100 da suka sace a wurare daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel