Gwamnan Zamfara Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha a Zaɓen Gwamnan Jihar

Gwamnan Zamfara Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha a Zaɓen Gwamnan Jihar

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, yace ya amince da kayen da ya sha a zaɓen gwamnan jihar
  • Gwamna Bello Matawalle ya sha kashi ne dai a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP, Dauda Lawal Dare
  • Gwamnan na Zamfara ya kuma nemi da mutanen jihar da su yafe masa kura-kuran da yayi musu

Jihar Zamfara- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya amince da kayan da ya sha a zaɓen gwamnan jihar. Rahoton Daily Trust

Gwamna Matawalle ya sha kashi ne a hannun ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Dauda Lawal Dare.

Matawalle
Gwamnan Zamfara Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha a Zaɓen Gwamnan Jihar Hoto: The Guardian
Asali: Twitter

A wani saƙon murya da ya aikewa mutanen jihar, gwamna Matawalle yace da shi da magoya bayan sa sun amince da hukuncin da Allah yayi, domin duk abinda ya faru haka ya ƙaddaro.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Naɗa Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki

Ya bayyana cewa lokacin da ya hau kan mulki ya tattauna da dukkanin wasu.masu ruwa da tsaki domin ganin an samo hanyoyin da za a samar da ɗauwamammen zaman lafiya a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya kuma ƙara da cewa har yanzu rashin tsaro shine kan gaba wajen abubuwan dake ci ma.jihar tuwo a ƙwarya. Rahoton Tribune

A kalamansa:

“Mun samu samu nasarar sasantawa a siyasance wanda hakan shiyasa aka yi yaƙin neman zaɓe cikin kwanciyar hankali, aka gudanar da tsaftatacciyar siyasa a jihar."
“Idan da sani na ko a rashin sani na ɓatawa wani, ina neman yafiyar sa. Ni ɗan Adam ne kamar kowa kuma Allah ne kawai babu kuskure a cikin lamuran sa."
“Ina son in kuma yi amfani da wannan damar wajen neman a zauna lafiya sannan na jajantawa waɗanda suka yi asarar kayayyakin su wajen yin murna. Yakamata mu san cewa ba mu da wani waje wanda ya wuce Zamfara."

Kara karanta wannan

Bayan Sake Komawa Kan Kujerar Sa, Gwamnan PDP Yayi Jawabi Mai Daukar Hankali Kan Masu Adawa Da Shi

"Ina kuma kira ga gwamnati mai zuwa da ta ƙoƙari wajen ganin ta dawo da zaman lafiya a jihar. Mun gode da jajircewa, aiki tuƙuru na al'ummar jihar mu."

Atiku Ya Garzaya Kotu, Ya Lissafo Hanyoyi 12 Da INEC Ta Taimaki Tinubu Ya Kayar Da Shi

A wani labarin na daban kuma, Atiku Abubakar ya bayyana hanyoyi 12 da INEC ta taimaka ya sha kashi a hannun Tinubu.

Atiku na jam'iyyar PDP dai yana ƙalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel