Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Coci, Sun sace Matarsa a Kaduna

Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Coci, Sun sace Matarsa a Kaduna

  • 'Yan bindiga sun halaka wani Malamin Coci kuma sun yi awon gaba da matarsa a jihar Kaduna
  • Shugaban CAN reshen jihar Kaduna, Joseph Hayab, ya ce 'yan ta'addan sun yi abun alheri, sun sako mutane 100 da ke hannunsu
  • Yace bayan zaben shugaban kasa, aka sace malamai uku kuma har yanzun ɗaya na hannun yan ta'adda

Kaduna - Wasu miyagun 'yan ta'adda sun halaka Rabaran Musa Mairimi, Malamin Cocin ECWA da ke Kasuwan Magani a karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna.

Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa (CAN) reshen Jihar Kaduna, Joseph Hayab, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Asabar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Matsalar tsaro a Kaduna.
Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Coci, Sun sace Matarsa a Kaduna Hoto: punch
Asali: UGC

Ya ce 'yan bindigan sun kutsa cikin ƙauyen ranar Alhamis, suka kashe Malamin Majami'ar, kana suka yi awon gaba da matarsa zuwa maɓoyarsu da ba'a sani ba.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Ceto Mutum 201 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Borno Da Kaduna

Sai dai ya ce labari mai daɗin ji shi ne 'yan ta'addan sun sako sama da mutane 100 da suka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na jihar Kaduna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hayab ya yi bayanin cewa sun gano an yi garkuwa da mutane sama da 100 kuma sun shafe sama da watanni Shida tsare a hannun yan ta'adda musamman a yankunan Kauru, Jaba, Kachia, Kagarko da Kajuru.

Har yanzu akwai wani Malami hannunsu - CAN

Bugu da ƙari, shugaban CAN a Kaduna ya kara da cewa daga gama zaɓen shugaban kasa, 'yan ta'adda suka sace Malaman Coci guda uku.

Ya ce maharan sun nemi a tara musu Miliyan N50m a matsayin kuɗin fansar ɗaya daga cikin Malaman, wanda har yanzun yana tsare a hannunsu.

Punch ta rahoto Hayab na cewa:

"Amma tattaunawar da aka fara da miliyan N50m yanzun ta dawo miliyan N5m. Wannan shi ne yanayin da muka tsinci kanmu a Kaduna."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro Sama da 50 a Jihar Zamfara

"Wa zaka tunkara, ko ka ruga gare shi da abinda ke damunka? Bayan duk wannan, tun da aka fara garkuwa da mutane a Kaduna, ba'a taba kama wani muhimmi ba har yau."

Gwamnan Jihar Sakkwato Ya Rasa Kwamshinan Harkokin Addinai

A wani labarin kuma Kwamishinan Harkokin Addinai A Jihar Sakkwato Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Alhaji Usman Suleiman (Ɗanmadamin Isa), ya rasu ne a Asibitin UDUS bayan fama da gajerun rashin lafiya yana da shekaru 72 a duniya.

Kafin rasuwarsa ya rike manyan mukamai kama daga shugaban PDP na jiha, ya rike ma'aikata akalla uku a matsayin kwamishina a Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel