Dan Takarar Gwamna Na NNPP A Taraba Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zabe, Ya Bayyana Matakinsa Na Gaba

Dan Takarar Gwamna Na NNPP A Taraba Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zabe, Ya Bayyana Matakinsa Na Gaba

  • Farfesa Sani Mohammed Yahaya, dan takarar gwamna na NNPP a jihar Taraba, a zaben ranar 18 ga watan Maris ya yi watsi da sakamakon zabe
  • Farfesa Yahaya ya ce sakamakon da INEC ta sanar ya banbanta da abin da aka samu a rumfunan zabe don haka zai shi kotu
  • A bangarensa, Sanata Emmanuel Bwacha dan tankarar gwamnan APC a jihar Taraba ya taya Agbu Kefas na PDP murnar cin zaben gwamnan

Jihar Taraba - Dan takarar gwamna na Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Farfesa Sani Mohammed Yahaya, ya yi watsi da sakamakon zaben gwamna da hukumar

Farfesa Yahaya, a ranar Laraba yayin martani kan sakamakon ya ce abin da aka fitar ba shine sakamakon da aka samu a rumfunan zabe ba, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara Ta Sanya Dokar Hana Fita Daga Wayewar Gari Zuwa Dare

Sani Yahaya
NNPP Ta Yi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Taraba, Ta Garzaya Kotu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da yasa dan takarar gwamnan Taraba na NNPP ya ki yarda da sakamakon zabe

Ya ce ya lashe zaben amma an murde sakamakon, ya kara da cewa mutanen jihar sun san cewa NNPP ne ta lashe zaben.

Dan takarar na NNPP ya bayyana cewa zai kallubalanci sakamakon zaben a kotu yana mai cewa ya tafi kotun don kwato nasararsa.

Ya yi kira ga magoya bayansa su kwantar da hankalunsa kuma kada su dauki doka a hannunsu.

Ya ce:

"Nasara ta mu ce, mun lashe zaben. Kowa a Jihar Taraba ya san hakan. Na ci zaben kuma za mu tafi kotu don kwato nasarar mu."

Dan takarar gwamna na APC ya taya Agbu Kefas murna

Amma shi dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Taraba, Sanata Emmanuel Bwacha ya taya Agbu Kefas na PDP murna, wanda shine INEC ta ayyana ya ci zabe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APC Ta Kwace Mulki Daga PDP, Babban Malami Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Arewa

Direktan watsa labarai na kwamitin kamfen din Sanata Bwacha, Mista Aaron Artimas, ya ce dan takarar gwamnan na APC ya amince da sakamakon zaben gwamnan kuma ya taya Kefas murna.

Ya ce Bwacha ya dauki matakin yin hakan ne saboda a samu zaman lafiya domin jihar na bukatar zaman lafiya da cigaba.

Hankula sun kwanta a Taraba

Hankulan mutane ya kwanta a Jalingo bayan INEC ta ayyana Kefas a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris a jihar.

Kasuwanci da aka dakatar bayan arangama tsakanin sojoji da yan sanda a Jalingo a ranar Litinin sun ci gaba.

Binciken ya nuna cewa, a ranar Litinin an sake bude kasuwanni da shaguna da aka rufe yayin da an rage adadin jami'an tsaro da aka baza a wasu wurare a garin.

Katsina: Ba mu yarda da sakamakon zaben gwamna ba, za mu tafi kotu, PDP

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

A wani rahoto mai kama da wannan, jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta yi fatali da sakamakon zaben gwamna na jihar da aka yi a ranar Asabar 18 ga watan Maris din 2023, tana mai cewa an tafka magudi iri daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel