Jerin Gwamnoni 9 Da Suka Samu Damar Yin Tazarce a Zaben 2023

Jerin Gwamnoni 9 Da Suka Samu Damar Yin Tazarce a Zaben 2023

An gudanar da zaɓen gwamnoni a faɗin tarayyar Najeriya a ranar 18 ga watan Maris 2023. An yi zaɓen gwamnonin ne a jihohi 28 na ƙasar nan.

Gwamnoni 11 suka fafata a zaɓen domin neman sake zarcewa kan kujerun su.

Ya zuwa yanzu hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana gwamnoni 9 a matsayin waɗanda suka sake zarcewa kan kujerun su, inda ya rage sauran jihar Adamawa kawai.

Gwamnoni
Jerin Gwamnoni 9 Da Suka Samu Damar Yin Tazarce a Zaben 2023 Hoto: Facebook
Asali: UGC

Ga jerin gwamnonin da suka samu yin tazarce:

1. Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Seyi Makinde na jam'iyyar PDP shine gwamnan farko da aka fara bayyanawa ya lashe zaɓe bayan ya samu ƙuri'u 563,756 inda ya lallasa abokin karawar sa Teslim Folarin na jam'iyyar APC, wanda ya samu ƙuri'u 256,685.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Gwamna a Jihar Borno

2. Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu

Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya samu nasara cikin sauƙi bayan ya samu ƙuri'u 762,134 inda ya lallasa abokin hamayyar sa na jam'iyyar Labour Party, Gbadebo Rhodes-Vivour wanda ya samu ƙuri'u 312,329.

3. Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun

Zaɓen gwamnan jihar Ogun yana ɗaya daga cikin wanda aka fafata sosai a cikin sa.

Sai dai, hukumar INEC ta bayyana gwamna Dapo Abiodun matsayin wanda ya samu nasara bayan ya samu ƙuri'u 276,298 inda doke abokin takarar sa na jam'iyyar PDP, Ladi Adebutu, wanda ya samu ƙuri'u 262,383.

4. Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya sake komawa kan kujerar sa bayan ya samu ƙuri'u 273,424 inda ya kayar da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Abdullah Yahman wanda ya samu ƙuri'u 155,490

5. Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya

Gwamna Inuwa Yahaya na jam'iyyar ya fuskanci adawa sosai a wajen sake komawa kan kujerar sa inda jam'iyyar PDP ta so ƙwace mulki a hannun sa.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar APC Ta Ƙara Lallasa PDP, Ya Lashe Zaben Gwamna a Ƙarin Wata Jihar

Sai dai gwamnan ya samu ƙuri'u 342,821 inda ya lallasa mai biye da shi Mohammed Jibrin Barde na jam'iyyar PDP, wanda ya samu ƙuri'u 233,131.

6. Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni

Gwamna Mai Mala Buni ya sake komawa kan kujerar sa cikin ruwan sanyi, bayan ya samu ƙuri'u 317,113 inda ya lallasa abokin hamayyar sa na jam'iyyar PDP, Sheriff Abdullahi wanda ya samu ƙuri'u 104,259.

7. Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed

Zaɓen jihar Bauchi yana ɗaya cikin waɗanda aka fafata sosai a cikin sa, sai dai gwamna mai ci Bala Mohammed na jam'iyyar PDP ya sake komawa kan kujerar sa.

Gwamnan ya samu ƙuri'u 525,280 inda yayi nasara akan ɗan takarar jam'iyyar APC, tsohon hafsan sojin sama, Sadique Abubakar wanda ya samu ƙuri'u 432,272.

8. Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule

Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC ya lallasa abokin takarar sa bayan ya samu ƙuri'u 347,209, yayin da David Ombugadu na jam'iyyar PDP ya samu ƙuri'u 283,016.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Tayi Hukunci a Zamfara Ta Lashe Kujerun Shugabannin Majalisar Dokokin Jihar

9. Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum

Gwamna Zulum ya sake komawa kan kujerar sa cikin ruwan sanyi bayan ya samu ƙuri'u 545,543 yayin da ɗan takarar PDP, Mohammed Jajari, ya zo na biyu da ƙuri'u 82,147.

Asali: Legit.ng

Online view pixel