2023: Dan Takarar APC Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Ebonyi

2023: Dan Takarar APC Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Ebonyi

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya lashe zaben gwamnan da aka kammala a jihar ranar Asabar
  • INEC ta ce ɗan takara a inuwar APC ya samu kuri'u mafi rinjaye wanda suka ba shi nasarar zama zababben gwamna
  • Shugaban majalisar zai maye gurbin gwamna David Umahi na APC wanda wa'adinsa na biyu zai ƙare a shekarar nan

Ebonyi - Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Honorabul Francis Nwifuru na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Ebonyi.

Rahoton Daily Trust ya ce Honorabul Nwifuru, wanda shi ne kakakin majalisar dokokin Ebonyi a halin yanzu, ya samu kuri'u 199,131.

Nwifuru Francis.
Zababben gwamnan jihar Ebonyi, Honorabul Nwifuru Francis Hoto: APCNigeria
Asali: Twitter

Babban abokin karawarsa da ke mara masa baya a matsayi na biyu, Mista Ifeanyichukwuma Odii, ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, ya tashi da kuri'u 80,191.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Sha Kaye, Jam'iyyar PDP Ta Lashe Zaben Gwamna a Wasu Ƙarin Jihohi 2

Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Farfesa Bernard Odo, ne ya zo na uku da ƙuri'u 52,189.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ni Farfesa Charles Igwe, bayan cikka dukkan matakan da aka sharɗa ma ayyana Nwifuru Francis a matsayin wanda ya samu nasara kuma ya zama zaɓaɓɓe," inji baturen zaben INEC.

Alkaluma sun nuna an ƙada kuri'u 342, 554 yayin da aka samu waɗanda suka lalace 7, 387 a jihar da ke kudu maso gabashim Najeriya.

The Cable ta tattaro cewa bayan wannan nasara, kakakin majalisar dokoki zai zama magajin da zai maye gurbin gwamna David Umahi.

Da yake jawabin amincewa da nasara, gwamna mai jiran gado ya ce sakamakon zaben ya nuna muradan mutanen jihar a fili.

Ya kuma ƙara da cewa ya sadaukar da dukkan biyayyarsa ga muradan mutanen jihar Ebonyi, waɗanda suka ga ya dace suka zaɓe shi a matsayin gwamna.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Kashi a Zaben Gwamna, Dan Takarar APC Yayi Wani Muhimmin Abu Daya Rak

Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP a Benuwai

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta samu nasarar kwace mulki hannun PDP a jihar Benuwai bayan INEC ta sanar da sakamako.

Babban Malamin Coci kuma ɗan takarar gwamna a inuwar APC ne ya samu kuri'u ma fi rinjaye a zaben da aka kammala ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel