Gwamna Babagana Zulum Ya Lashe Zaben Da Yake Neman Tazarce a Borno

Gwamna Babagana Zulum Ya Lashe Zaben Da Yake Neman Tazarce a Borno

  • Farfesa Babagana Umaru Zulum ya samu nasarar cika burinsa na tazarce a kan kujerar gwamna a jihar Borno
  • INEC ta ayyana Zulum, ɗan takara a inuwar jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar
  • Bayan haka, APC ta lashe baki ɗaya kujerun mambobin majalisar dokokin Borno guda 28

Borno - Gwamna Babagana Umaru Zulum ya lashe zaben gwamna karo na biyu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Farfesa Zulum, ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC, ya samu nasara ne bayan kammala tattara sakamakon zaben gwamna wanda ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Babagana Umaru Zulum.
Gwamna Babagana Zulum Ya Lashe Zaben Da Yake Neman Tazarce a Borno Hoto: Zulum
Asali: UGC

Baturen zaben da INEC ta ɗora wa alhakin tattara sakamakon jihar Borno, Jude Rabo, ne ya sanar da wanda ya ci zaben da yammacin ranar Litinin 20 ga watan Maris, 2023.

Ya ce gwamna mai ci kuma ɗan takara a inuwar APC, Farfesa Zulum, ya samu kuri'u 545,542, wanda ya ba shi damar lallasa babban abokin karawarsa na jam'iyar PDP, Mohammed Jajari, mai kuri'u 82,147.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

The Cable ta tattaro cewa gwamna Zulum ya samu nasara kan sauran tawarorinsa na jam'iyyu daban-daban 11 da suka shiga tsere.

Bugu da ƙari, jam'iyyar APC ta lashe kujerun mambobin majalisar dokokin jihar Borno guda 28 a zaben wanda ya gudana ranar Asabar da ta gabata.

Daga cikin waɗanda suka samu naaarar komawa majalisar har da kakakin majalisaɗ na yanzu, Abdulkarim Lawan, wanda shi ne mafi daɗewa, karo na biyar kenan.

Zulum ya gaji ɗare kujerar gwamnan jihar Borno daga hannun mataimakin shugaban ƙasa mai jiran gado, Sanata Ƙashim Shettima.

Kawo yanzu jam'iyyar APC ke kan gaba da yawan kujerun gwamnoni, yayin da jam'iyyar PDP ke biye mata baya.

Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP, Ta Kwace Mulkin Jihar Benuwai

A wani labarin kuma Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a Benuwai.

Babban malamin coci kuma ɗan takarar gwamna a inuwar APC ya samu nasarar lallasa babban abokin karawarsa na PDP da kuri'u mafi rinjaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel