An Yi Awon Gaba da Jami’an Hukumar Zaben da Suka Dauko Sakamako Daga Maradun Ta Zamfara

An Yi Awon Gaba da Jami’an Hukumar Zaben da Suka Dauko Sakamako Daga Maradun Ta Zamfara

  • Rahoton da muke samu daga jihar Zamfara mai ban tsoro na cewa, an sace wasu daga cikin jami'an tattara sakamakon zaben gwamna a jihar
  • An sace jami'an biyu a hanyarsu ta zuwa hedkwatar hukumar da ke Gusau don ba da sakamakon zaben karamar hukumar Muradun
  • Ya zuwa yanzu, ba a kammala tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Zamfara da ke Arewa masu Yammacin Najeriya

Jihar Zamfara - Yanzu muke samun labarin cewa, an sace jami’an hukumar zabe ta INEC a yankin karamar hukumar Maradun da ke jihar jihar Zamfara.

Maradun ne karamar hukumar da gwamna Bello Matawalle ya fito, wanda shine gwamnan jihar da ke neman a sake zabansa a karo na biyu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an sace jami’an ne a hanyarsu ta zuwa hedkwatar INEC da ke Gusa don kai sakamakon zaben karamar hukumar ta Maradun.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APC Ta Kwace Mulki Daga PDP, Babban Malami Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Arewa

An sace jami'an INEC a Zamfara
Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Matakin da ake dauka kan lamarin

Jami'in hulda da jama'a na hukumar INEC a jihar, Muktari Janyau ya shaidawa majiya cewa, tuni an kai batun gaban 'yan sanda.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Kwamishinan aikin zabe mai kula da jihar Zamfara, Farfesa Sa'idu Babura Ahmed ya kai rahoton lamarin ga kwamishinan 'yan sanda don daukar matakin da ya dace."

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 14 na jihar ta Zamfara, inda aka sanar da na kananan hukumomi 9.

A halin da ake ciki, jam'iyyar PDP mai son tumbuke gwamnan mai ci ne ke kan gaba a wannan zaben da aka gwabza a karshen makon jiya.

A sako wadanda aka sace

Sai dai, bayan wani dan lokaci rahoton jaridar Daily Trust ya kara da cewa, an sako jami'an biyu da aka sace a jihar.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar APC Ta Ƙara Lallasa PDP, Ya Lashe Zaben Gwamna a Ƙarin Wata Jihar

Ya zuwa yanzu ba a bayyana dalilin sace su ba, kana ba a san abubuwan da aka tattauna dasu ba kafin sako su.

INEC bata amince da sakamakon zaben jihar Adamawa ba

A wani labarin kuma, kun ji yadda hukumar zabe ta INEC tace sam bata amince sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa ba.

Hukumar ta bayyana hakan ne bayan bayyana sakamakon karamar hukumar karshe a jihar.

A jihar, gwamnan PDP ne ke neman komawa mulki, yayin da Aisha Binani, 'yar takarar APC ke son karbe kujerar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel