"Zan Yi Aiki Tare Da Bola Tinubu" Gwamna Makinde Ya Sha Alwashi

"Zan Yi Aiki Tare Da Bola Tinubu" Gwamna Makinde Ya Sha Alwashi

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sha alwashin yin aiki hannu da hannu tare da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu
  • Gwamnan ya bayyana cewa za suyi aiki tuƙuru wajen ganin sun ɗinke ɓaraka tare da samar da haɗin kai a tsakanin ƴan Najeriya
  • Gwamna Seyi Makinde yana daga cikin gwamnonin da suka samu nasarar sake lashe zaɓen su a zaɓen gwamnoni na shekarar 2023

Jihar Oyo- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo yayi alƙawarin yin aiki hannu da hannu tare da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, idan aka tsantsar da gwamnatin sa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Gwamna Makinde yayi wannan alƙawarin ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na TVC a ranar Lahadi. Rahoton Vanguard

Makinde
"Zan Yi Aiki Tare Da Bola Tinubu" Gwamna Makinde Ya Sha Alwashi Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa zasu aiki wajen ganin cewa sun haɗa kan ƴan Najeriya sannan ana ba kowa dama daga ƙasar ba tare da la'akari daga wane yanki ya fito ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rikici Ya Kara Tsananta a Kano, An Wargaza Akwatunan Zabe Sama da 10

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Zan yi aiki tare da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa. Za mu cigaba da aiki tare wajen tabbatar da cewa mun samar da haɗin kai a Najeriya. Za mu tabbatar da cewa Najeriya na kan turbar ba kowa dama. Za mu aiki da son ganin mun ɗaga darajar ƙasar mu Najeriya.

Makinde Ya sake komawa kan kujerar sa

Idan ba a manta ba dai hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), tun da farko ta bayyana a hukumance cewa gwamna Seyi Makinde shine ya lashe zaɓen gwamnan jihar Oyo. Rahoton Premium Times

Makinde na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu ƙuri'u 563,617 yayin abokin hamayyar sa mai take masa baya Sanata Teslim Folarin na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu ƙuri'u 251,230.

Adebayo Adelabu na jam'iyyar Accord Party (AP) ya zo na uku inda ya samu ƙuri'u 38,757.

Kara karanta wannan

"Mutuwa Ce Makomar Duk Mai Son Tayar Da Rikici a Ranar Zabe", 'Yan Sanda

Ahmed Aliyu Na APC Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Sokoto

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta samu nasara a zaɓen gwamnan jihar Sokoto.

Jam'iyyat APC ta karɓe mulkin jihar daga hannun jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel