Rundunar 'Yan Sanda Tayi Kakkausan Gargadi Ga Masu Son Kawo Hargitsi Ranar Zabe

Rundunar 'Yan Sanda Tayi Kakkausan Gargadi Ga Masu Son Kawo Hargitsi Ranar Zabe

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya tayi gargaɗi mai zafi kan masu niyyar tayar da hatsaniya a ranar zaɓe
  • Mataimakin sufeto janar na ƴan sanda na shiyyar Kudu maso Gabas ya bayyana cewa masu son tayar da rikici su shirya komawa ga mahaliccin su
  • Ya kuma bayar da tabbacin cewa rundunar a shirye take domin bayar da cikakken tsaro a zaɓen

Jihar Abia- Rundunar ƴan sandan Najeriya (NPF), tayi kakkausan gargaɗi kan maso son tada hatsaniya a zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokoki na ranar Asabar.

A yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnonin, ana zaman ɗar-ɗar a tsakanin jam'iyyu da magoya bayan su kan yiwuwar ɓarkewar rikici a ranar zaɓen.

Yan Sanda
Rundunar 'Yan Sanda Tayi Kakkausan Gargadi Ga Masu Son Kawo Hargitsi Ranar Zabe Hoto: The Cable
Asali: UGC

Mataimakin sufeto janar na ƴan sanda mai kula da yankin Kudu maso Gabas, John Amadi, yayi kira ga mutanen yankin da kada su yarda a sanya musu wata fargaba a rai. Rahoton The Cable

Kara karanta wannan

"Ƴan Najeriya Basu Taba Zabe Cikin Kwanciyar Hankali Kamar Na Bana Ba", Garba Shehu Ya Magantu

“Ƴan sanda na nan domin bayar da kariya." A cewar sa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Duk wanda yake son sanya kan shi cikin matsala ko ya shiga cikin daba to ya kuka da kan shi. Duk wanda yayi ƙoƙacin satar akwati ko tayar da hatsaniya wajen zaɓe zai fuskanci fushin hukuma."
"Duk wanda yake son tayar da hatsaniya to ya shirya mutuwa sannan duk wanda yake son mutuwa to ya zo ya tayar da hatsaniya. Idan kana son rayuwar ka, ka kaɗa ƙuri'a ka koma gida kawai ka jira sakamako."
Mataimakin sufeto janar din yayi kira ga mutanen jihar da su yi watsi da kowace irin barazanar hana gudanar da zaɓen, inda ya ƙara da cewa za a ba jami'an hukumar INEC cikakkiyar kariya. Rahoton PM News

Ya bayar da tabbacin rundunar na shiryawa tsaf domin zama tsaka tsaki a lokacin zaɓen, inda yake cewa rundunar ƴan sandan bata da wata jam'iyya.

Kara karanta wannan

"Har Yanzu Kwankwaso Amini Na Ne" Gwamna Ganduje Ya Bayyana Dangantakarsa Da Kwankwaso

Jam'iyyar NNPP Ta Janye Zanga-Zangar Lumana Kan DSS A Kano

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta janye zanga-zangar lumana da ta shirya kan hukumar DSS a jihar.

Jam'iyyar tana zargin hukumar da nuna mata wariya da ƙoƙarin kawo mata cikas a ranar zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel