Yanzu Yanzu: INEC Ta Ayyana Makinde a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Oyo

Yanzu Yanzu: INEC Ta Ayyana Makinde a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Oyo

  • A karshe an samu wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Oyo na 2023 wanda aka fafata tsakanin Seyi Makinde da Teslim Folarin
  • Adebayo Bamire, baturen zabe, ya ayyana Gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Maris
  • A cewar Bamire, dan takarar PDP ya samu kuri’u 563,756 yayin da babban abokin hamayyarsa na APC ya samu 256,685

Oyo - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Seyi Makinde a mnatsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Oyo, jaridar The Cable ta rahoto.

Makinde wanda ya kasance dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yi nasarar lashe zaben gwamna a karo na biyu.

Yan takarar PDP da APC a zaben gwamnan Oyo
Yanzu Yanzu: INEC Ta Ayyana Makinde a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Oyo Hoto: Seyi Makinde, Teslim Folarin
Asali: Facebook

Dan takarar na PDP ya lashe kananan hukumomi 31 cikin 33 da jami’an tattara sakamakon zabe suka sanar a ofishin INEC da ke Ibadan, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC Ta Yi Kasa-Kasa Da PDP a Zaben Majalisar Ekiti, Ta Lashe Kujeru 23

Gwamna Makinde ya samu kuri'u 563,756 wajen lallasa Teslim Folarin na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya samu kuri'u 256,685, yayin da Adebayo Adelabu na jam'iyyar Accord Party ya samu kuri'u 38,357.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Asabar, 18 ga watan Maris ne dai aka gudanar da zabukan gwamnoni da na yan majalisar jihohi a fadin jihohi 28 cikin 36 na kasar.

Yawan kuri'un da kowani dan takara ya samu

Accord Party - 38,357

APC - 256,685

Labour Party - 1500

PDP - 563,756

Jimilar kuri'u masu inganci - 874,672

Lalatattun kuri'u - 14,920

Jimilar kuri'un da aka kada - 889,592

APC ta lashe mafi rinjayen kujeru a majalisar dokokin jihar Ekiti

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe mafi rinjayen kujeru na yan majalisa a majalisar dokokin jihar Ekiti a zaben da aka yi na ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC Ta Lashe Kujeru 22 Cikin 26 Na Majalisar jiha a Ondo

Yayin da jam'iyyar APC ke da kujeru 23, Social Democratic Party (SDP) ta yi nasarar lashe kujeru biyu inda babban jam'iyyar adawar kasar ta Peoples Democratic Party (PDP) ta kasa samun ko guda daya.

An kuma ayyana kujerar mazaba guda daya a matsayin ba kamalalle ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel