Zaben 2023: PDP Ta Sha Mummunan Kaye Yayin da APC Ta Lashe Kujeru 23 a Majalisar Ekiti

Zaben 2023: PDP Ta Sha Mummunan Kaye Yayin da APC Ta Lashe Kujeru 23 a Majalisar Ekiti

  • A ranar Asabar, 18 ga watan Maris ne aka gudanar da zaben gwamnoni da na majalisar jihohi
  • Jam'iyyar APC mai mulki ta lashe kujerun yan majalisar dokoki guda 23 a jihar Ekiti a zaben
  • PDP bata samu kujera ko daya ba yayin da SDP ke da guda biyu an kuma ayyana daya a matsayin ba kamallale ba

Ekiti - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasarar lashe kujeru 23 a majalisar dokokin jihar Ekiti a zaben da aka yi ranar Asabar, 18 ga watan Maris, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta lashe kujeru biyu a mazabun Ekiti East 1 da Ise/Orin yayin da aka ayyana kujerar Ido/Osi 1a matsayin ba kammalalle ba.

Logon jam'iyyar APC mai mulki a kasar
Zaben 2023: PDP Ta Sha Mummunan Kaye Yayin da APC Ta Lashe Kujeru 23 a Majalisar Ekiti Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kamar yadda ya bayyana a sakamakon zaben da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta saki, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bata lashe kowace kujera ba a zaben na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC Ta Lashe Kujeru 22 Cikin 26 Na Majalisar jiha a Ondo

Mista Temitope Akanmu, shugaban sashin wayar da kan masu zabe da hulda da jama'a shine ya saki sakamakon zaben a madadin kwamishinan zabe na yankin, Farfesa Ayobami Salami.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalilin ayyana zaben mazabar Ido/Osi 1 a matsayin ba kammalalle ba

Hukumar INEC ta ce zaben mazabar Ido/Osi 1 ya zama ba kammalalle bane saboda tazarar da ke tsakanin yan takara da kuma bukatar yin zaben cike gurbi a rumfunan zabe uku kafin a samu wanda ya yi nasara.

Hukumar ta kara da cewa:

"Hakan ya kasance ne sakamakon rikici da hargitsi da aka samu a tsarin zaben a PU 003, PU 012 da PU 014 a gudunma ta 01."

A halin da ake ciki, Farfesa Ayobami Salami ya ce an yi zaben jihar Ekiti cikin lumana illa rashin fitowar mutane da dama wajen kada kuri'un, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Ba Za Ku Iya Kwace Wa Tinubu Nasarsa Ba, APC Ta Yi Martani Ga Obi

APC ta lashe kujeru 22 cikin 26 na majalisar Ondo

A wani lamari makamancin wannan, mun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta yi nasarar lashe kujeru 22 a majalisar dokokin jihar Ondo a zaben Asabar, 18 ga watan Maris.

Babbar jam'iyyar PDP mai adawa ta tashi da sauran kujerun guda hudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel