Yanzu Yanzu: INEC Ta Ayyana Makinde a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Oyo
- A karshe an samu wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Oyo na 2023 wanda aka fafata tsakanin Seyi Makinde da Teslim Folarin
- Adebayo Bamire, baturen zabe, ya ayyana Gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Maris
- A cewar Bamire, dan takarar PDP ya samu kuri’u 563,756 yayin da babban abokin hamayyarsa na APC ya samu 256,685
Oyo - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Seyi Makinde a mnatsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Oyo, jaridar The Cable ta rahoto.
Makinde wanda ya kasance dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yi nasarar lashe zaben gwamna a karo na biyu.
Dan takarar na PDP ya lashe kananan hukumomi 31 cikin 33 da jami’an tattara sakamakon zabe suka sanar a ofishin INEC da ke Ibadan, rahoton Nigerian Tribune.
Gwamna Makinde ya samu kuri'u 563,756 wajen lallasa Teslim Folarin na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya samu kuri'u 256,685, yayin da Adebayo Adelabu na jam'iyyar Accord Party ya samu kuri'u 38,357.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Asabar, 18 ga watan Maris ne dai aka gudanar da zabukan gwamnoni da na yan majalisar jihohi a fadin jihohi 28 cikin 36 na kasar.
Yawan kuri'un da kowani dan takara ya samu
Accord Party - 38,357
APC - 256,685
Labour Party - 1500
PDP - 563,756
Jimilar kuri'u masu inganci - 874,672
Lalatattun kuri'u - 14,920
Jimilar kuri'un da aka kada - 889,592
APC ta lashe mafi rinjayen kujeru a majalisar dokokin jihar Ekiti
A wani labarin kuma, mun ji cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe mafi rinjayen kujeru na yan majalisa a majalisar dokokin jihar Ekiti a zaben da aka yi na ranar Asabar, 18 ga watan Maris.
Yayin da jam'iyyar APC ke da kujeru 23, Social Democratic Party (SDP) ta yi nasarar lashe kujeru biyu inda babban jam'iyyar adawar kasar ta Peoples Democratic Party (PDP) ta kasa samun ko guda daya.
An kuma ayyana kujerar mazaba guda daya a matsayin ba kamalalle ba.
Asali: Legit.ng