Zaben 2023: Abin da Nake Ji Idan Limamin Juma'a Ya Yi Addu'ar Allah-tsine Ga 'Yan Murdiyar Zabe

Zaben 2023: Abin da Nake Ji Idan Limamin Juma'a Ya Yi Addu'ar Allah-tsine Ga 'Yan Murdiyar Zabe

  • Sanata Shehu Sani ya magantu yayin da yan Najeriya ke shirin zaben sabbin gwamnoni a jihohinsu
  • Tsohon Sanatan ya ce wani limami ya yi tofin Allah tsine ga wadanda ke shirin yin murdiya a zaben
  • Sai dai a cewar Sani ya ji mamaki da ya ga yawancin mutane sun ki cewa 'Amin' a masallacin na Juma'a

Tsohon sanata wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya bayyana wani abun mamaki da ya ci karo da shi a masallaci a ranar Juma'a, 17 ga watan Maris.

Sani ya ce Limamin masallacin ya yi addu'a kan wadanda ke shirin yin magudi a zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani
Zaben 2023: Abin da Nake Ji Idan Limamin Juma'a Ya Yi Addu'ar Allah-tsine Ga 'Yan Murdiyar Zabe
Asali: UGC

Sai dai kuma, tsohon dan majalisar ya ce ya sha mamaki da ganin yanayin wasu mutane.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: "Za Mu Kashe Duk Wanda Ya Shirya Mutuwa a Yau" – Yan Sanda Sun Gargadi Masu Tada Zaune Tsaye

Yayin da yan Najeriya ke duba zuwa ga zaben na ranar Asabar, Sani ya bayyana cewa Limamin masallacin ya yi addu'a kan azabar Allah ta sauka a kan wadanda ke shirin yin magudi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, Sanatan ya ce ga mamakinsa, wasu mutane sun ki su ce 'Amin' ga addu'an da wannan Limami ya yi.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter:

"A yau a masallacin Juma'a, wani Limami ya yi addu'a kan azabar Allah ta tabbata ga wadanda ke son yin magudi a zaben gwamnoni a gobe, na lura cewa wasu sun ki amsawa da 'Amin'."

Jama'a sun yi martani

@IUmunwa ya yi martani:

"Ta yaya za su ce 'Amin' kan abun da suke son yi ."

@LawrenceOkoroPG ya ce:

"Zamu hada muryoyinmu wajen ihun Amennnnnnnnnnnnnnnnnnnn da karfi."

@krazycoozy:

"Allah ya biya Comrade Sai Hashiru"

Kara karanta wannan

'Dan takaran Sanatan APC a Kaduna Zai Tafi Kotu, Ya Fito da Hujjojin Magudin PDP

@Titilay2020:

"Allah ya ji addu'o'in kuma ya amsa! Fadin amin dinsu ko rashin fadi baya nufin komai."

@nasty_deo ya ce:

"Amin a madadinsu."

@abduoljg ya yi martani:

"Amen ya Allah."

@teekhaldum ya ce:

"A massalacin nagwamutse tu shima Ashiru da kai bakuce ameen ba agaban mu akayi."

@katomarthanyam1 ya ce:

"Allah yayi mama mai kyau."

Duk wanda ya shirya mutuwa ya zo hargitsa zabe, yan sanda

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar yan sanda ta gargadi jama'a da ke shirin kawo hargitsi a yayin zaben gwamnoni da yan majalisar jihohi cewa za su dandana kudarssu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel