Barau Jibrin Ya Shiga Takarar Kujerar Shugaban Majalisa, Ya Gana Da Zababbun Sanatoci 70

Barau Jibrin Ya Shiga Takarar Kujerar Shugaban Majalisa, Ya Gana Da Zababbun Sanatoci 70

  • Bayan zaben gama gari, yan majalisa sun fara shirye-shiryen na su zaben na cikin gida a Abuja
  • Hasali ana gudanar da zaben shugabannin majalisar dokokin tarayya a watan Yuni bayan shigan sabon shugaban kasa ofis
  • An fara rade-radin cewa tunda Tinubu da Shettima Musulmai ne, wajibi a baiwa Kirista shugabancin majalisa

Sanata mai wakiltan mazabar Kano ta Arewa a majalisar dattawa kuma zababben Sanata, Alhaji Barau Jibrin, ya zanna da sabbin Sanatoci 70 don tattaunawa da su gabanin zaben shugabannin majalisa.

TheNation ta ruwaito cewa Barau Jibrin na cikin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10.

An tattaro cewa akalla zababbun sanatoci 70 ne suka halarci zaman da akayi a NICON Luxury Hotel, Abuja ranar Talata.

Barau Jibin
Barau Jibrin Ya Shiga Takarar Kujerar Shugaban Majalisa Hoto: Hira
Asali: UGC

Rahoton ya ce an kwashe sa'a guda ana tattaunawa kuma Barau Jibrin ya bayyana cewa an shirya zaman ne domin sabbin yan majalisan su san juna gabanin rantsar da majalisar.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya: Kwankwaso Ya Karbi Bakuncin Mutum 17 Da Suka Samu Nasara a Zaben Majalisa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Barau Jibrin ne Sanata guda daya tilo da ya sha a guguwar jam'iyyar NNPP da ta nade kujerun majalisar jihar Kano.

Wani zababben Sanata daga yankin kudu wanda ya halarci zaman ya ce ba yan jam'iyyar APC kadai suka halarta ba, har da sauran jam'iyyu hamayya.

A cewarsa:

"A matsayina na Sanata mai zuwa majalisa karo na biyu, na san Barau saboda na yi hulda da shi."
"Ya fahimci yadda abubuwa ke gudana a majalisa kuma mutum ne mai saukin kai."
"Zan zabeshi a watan Yuni lokacin rantsar da majalisa ta 10."

Wani sanatan daban shima daga kudancin Najeriya wanda zabon shiga majalisa ne yace:

"Ko shakka babu Barau Jibrin zan zaba matsayin shugaban majalisa, dan majalisa ne mai kirki kuma ya iya jagoranci."

Wani hadimin Barau Jibrin ya bayyana cewa Sanatan ya shirya zaman ne domin tattauna da takwarorinsa.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisa Ya Ki Karbar Satifiket Din INEC, Yana Harin Mukami Kusa da Tinubu

A cewarsa:

"An shirya zaman ne domin ya samu damar tattaunawa da sanayya tsakaninsa da takwarorinsa, babu komai sabanin haka."

Bayan ranar da shugaban kasa ranar 29 ga Mayu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai tura wasika a watan Yuni majalisa na rantsar da su.

Hakan zai basu damar zaben shugabanninsu.

Jam'iyyar APC na shawaran baiwa yankin Igbo shugabancin majalisar dattawa

Wata Majiya ta bayyana cewa tun Bola Ahmed Tinubu, zababben shugaban kasa Musulmi ne, mataimakin sa daga Arewa Musulmi ne, ya kamata a miƙawa mutanen Kirista kuma kudu shugaban majalisar dattawan

Asali: Legit.ng

Online view pixel