Shugaban Majalisa Ya Ki Karbar Satifiket Din INEC, Yana Harin Mukami Kusa da Tinubu

Shugaban Majalisa Ya Ki Karbar Satifiket Din INEC, Yana Harin Mukami Kusa da Tinubu

  • Shugaban majalisar wakilan tarayyar bai cikin wadanda suka je karbar shaidar lashe zaben 2023
  • Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya sake cin zabe a mazabar Surulere I, amma da alama zai yafe kujerar
  • Idan jita-jitar da ke yawo ta tabbata, Gbajabiamila zai samu mukami a fadar shugaban kasa

Abuja - Shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila bai cikin wadanda suka je dakin taron ICC domin karbar takardar shaidar cin zabe.

Leadership a wani rahoto da ta fitar, ta ce ba a ga Rt. Hon. Femi Gbajabiamila a sahun zababbun ‘yan majalisar kasar da INEC ta mikawa satifiket ba.

Duk da ya lashe zaben 2023 domin ya wakilci mazabar Surulere I da ke jihar Legas a karo na biyar, ana tunanin shugaban majalisar ya yafe kujerarsa.

Ganin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai zama shugaban kasa, kuma yana cikin na hannun dama, da alama Gbajabiamila yana harin kujera mai tsoka.

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

Dama ta samu a Gwamnati

Wani rahoton ya nuna shugaban majalisar wakilan yana so a nada shi ya zama shugaban ma’aikatan fadar Aso Rock idan an canza gwamnati.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa ‘dan majalisar na Legas yana cikin wadanda ya yi wa Bola Tinubu biyayya na fiye da tsawon shekaru 20 a siyasa.

Shugaban Majalisa
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Twitter

Kishin-kishin yana ta yawo

Wadanda ke tare da shugaban majalisar sun tabbatar da cewa su na samun kishin-kishin, Gbajabiamila zai fasa zarcewa a majalisa, ya shiga fada,

"Idan kun lura bai je karbar satifiket din samun nasara a ranar Laraba ba, maganar gaskiya bai bukatar satifiket dinnan.
Femi Gbajabiamila yana da duk abin da ake bukata domin ya zama shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnati a Najeriya.
Ya yi aiki da ‘yan siyasa a duka mazabun tarayya a yankunan kasar nan a shekaru 20 da suka wuce.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta mamayi Shugaban Kasa, an daga zaben Gwamnoni bai da labari

- Wata majiya

Da aka tuntubi Hadimin ‘dan siyasar game da batun, Lanre Lasisi bai iya cewa komai ba, iyaka ya ce mai gidansa bai samu damar zuwa dakin taron ICC ba.

Bisa al’ada, shugabanni su na zaban na-kusa da su domin su kula da fadar Aso Rock Villa. Da Buhari ya hau mulki a 2015, sai ya jawo Malam Abba Kyari.

Tseren zama sabon Shugaban majalisa

A wani rahotonmu, kun ji ana tunanin Alhassan Ado Doguwa yana sha’awar zama Shugaban majalisa, sai dai yanzu ana shari'a da shi a gaban kotu.

Aminu Jaji ya dawo majalisa da karfinsa, watakila ya gwabza da Ahmed Idris Wase da Muktar Aliyu Betara a wajen gaje kujerar Femi Gbajabiamila.

Asali: Legit.ng

Online view pixel