Gwamna Uzodinma Ya Tsige Kwamishinan Kwadugo Kan Rikicin NLC

Gwamna Uzodinma Ya Tsige Kwamishinan Kwadugo Kan Rikicin NLC

  • Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya kori kwamishinan kwadugo da samarwa na jihar, Ford Ozumba, daga mukaminsa
  • Hakan na kunshe a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya fitar yau Asabar 11 ga watan Maris, ya ce matakin zai kama aiki nan take
  • Bayanai sun nuna cewa Uzodinma ya raba kwamishinan da aikinsa ne saboda takun saƙan da gwamnatinsa ta fara da NLC

Imo State - Gwamnan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, Hope Uzodinma, ya tsige kwamishinan kwadugo da harkokin samarwa, Ford Ozumba, daga kan kujerarsa.

Kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin jihar, Declan Emelumba, shi ne ya tabbatar da korar kwamiahinan a wata sanarwa da ya aike wa Channels tv ranar Asabar 11 ga watan Maris, 2023.

Ford Ozumba.
Kwamishinan kwadugo na jihar Imo, Ford Ozumba. Hoto: channelstv
Asali: UGC

A sanarwan, gwamna Uzodinma, mamban jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan, ya ce matakin tsige kwamishinan zai fara aiki nan take.

Bayanai sun nuna cewa gwamnan ya umarci Mista Ford Ozumba, ya miƙa dukkan takardu da kayan da ke hannunsa ga Sakataren ma'aikatar kwadugo da samarwa nan take.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Meyasa Uzodinma ya kori kwamishinan daga aiki?

Sanarwan ba ta bayyana asalin abinda ya sa gwamnan ya ɗauki matakin korar kwamishinan ba, kamar yadda jaridar Tribune online ta ruwaito.

Amma wasu majiyoyi sun nuna cewa gwamna ya sallami kwamishinan ne saboda zaman doya da manjan da ya shiga tsakanin ƙungiyar kwadugo (NLC) ƙarƙashin shugabanta, Joe Ajaero, da gwamnatin jihar Imo.

A ranar Asabar mai zuwa 18 ga watan Maris, 2023, za'a gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya bayan tsaikon da aka samu wanda ya kai ga ƙara mako guda.

Gwamna Dapo Abiodun Ya Ce LP Ta Dawo Bayansa

A wani labarin kuma Hankalin PDP Ya Tashi, APC Ta Samu Gagarumin Goyon Bayan da Zai Ba Ta Nasara a Zabe Na Gaba a Ogun

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta samu babban nasara sakamakon matakin da shugabannin Labour Party suka ɗauka gabanin ranar zaɓe.

Ya ce mambobin kwamitin zartaswa na LP a Ogun tare da manyan jagororinsu sun amince so goya masa baya ya ci gaba da mulki a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel