Radda VS Lado: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Yan Takara 2 a Katsina

Radda VS Lado: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Yan Takara 2 a Katsina

Bayan tsaikon da aka samu, ranar 18 ga watan Maris, 2023, Katsinawa zasu fita rumfunan zaɓe domin zaɓen wanda su ke ganin ya dace ya zama gwamnan Katsina.

Daga cikin 'yan takarar da ke neman kujerar gwamnan jihar, Legit.ng Hausa ta ɗauki fitattu guda biyu da zata hasko muku wasu muhimman abubuwa game da su.

Dakta Dikko Umaru Radda, mai neman zama gwamna a inuwa APC da abokin karawarsa na PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗan-Marke, su ne ake ganin sun fi damar samun nasara.

Dikko Radda na APC

Cikakken sunansa shi ne, Dikko Umaru Radda, kuma shi ne ɗan takarar gwamna a inuwar APC mai mulki a jihar Katsina. Mun tattara muku abubuwan da ya dace ku sani game da shi kamar haka;

1. An haifi Dikko ranar 10 ga watan Satumba, 1969 a garin Hayin Gada da ke yankin ƙaramar hukumar Dutsin-ma, jihar Katsina, arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Shiga Neman Tsohon Gwamna Kan ‘Kisan Kai da Garkuwa da Mutane’

2. Ya yi karatunsa na Firamare a garin Radda, daga nan ya wuce kwalejin horad da Malamai a Zariya. Tsakanin 1986-1989, Raɗɗa ya samu shaidar koyarwa a kwalejin Ilimi ta Kafanchan (FCE).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dakta Dikko Radda.
Tsohon shugaban SMEDAN, Dikko Radda Hoto: Dikko Radda
Asali: Facebook

3. Dikko ya yi digiransa na farko a jami'ar Tafawa Balewa dake Bauchi (ATBU) a fannin fasahar noma da kiyo. Ya shiga jami'ar ABU Zariya ya samu shaidar digiri na biyu.

4. A 2005 ya sake komawa ABU ya yi karatun digiri na biyu a fannin International Affairs and Diplomacy daga bisani ya koma jami'ar a 2015 ya ƙarisa karatun digirin digirgir watau Ph.D a fannin noma.

5. Ya yi aikin koyarwa kana ya yi aikin Banki a tsakanin 1999 zuwa 2003 kafin daga bisani ya shiga harkokin siyasa ka'in da na'in.

6. Raɗɗa ya rike kujerar shugaban ƙaramar hukumar Charanchi daga 2005 zuwa 2007. An sake zaɓensa a matsayin Kantoman Charanci.

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna 3 da Aka Raina Kuma Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni

7. Ya riƙe mukamin Sakataren walwala da jin daɗi na jam'iyyar APC ta ƙasa daga 2014 zuwa 2015.

8. Gwamna Aminu Bello Masari ya naɗa shi shugaban ma'aikatan fadar gwamnati bayan guguwar canji ta baiwa APC nasara a jihar Katsina.

9. Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nada Dikko Radda a matsayin shugaban hukumar kula da kanana da matsakaitan masana'antu (SMEDAN) har sau biyu.

10. Shi ne Gwagwaren Katsina, Sarautar da Masarautar Katsina ta naɗa masa.

11. A halin yanzun shi ne ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a inuwar APC mai mulki bayan samun nasara a zaben fidda gwanin da ya gudana a watan Mayu, 2022.

Sanata Yakubu Lado na PDP

Akwai abubuwa masu tarin yawa game da ɗan takarar gwamnan Katsina na PDP, Sanata Yakubu Lado, mun tsinto muku muhimmai daga cikisu kamar haka;

1. An haifi Garba Yakubu a shekarar 1961 a ƙauyen da ake kira Ɗanmarke, karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

APC Na Tsaka Mai Wuya, Ɗan Takarar Gwamna Ya Janye Daga Takara Kwana 4 Gabanin Zabe

2. Ya yi karatun Firamare a Danmarke da Sakandire a kwalejin gwamnatin Katsina. Ya karanci kwas din Management & Finance a kwalejin fasaha watau Kaduna Poly.

Sanata Yakubu Lado.
Yakubu Lado tare da Atiku Abubakar Hoto: Suleiman abdullahi/facebook
Asali: Facebook

3. Yakubu Lado ya rike shugaban ƙaramar hukumar Kankara daga 1999-2002. Ya zauna a kujerar mamban majalisar wakilan tarayya daga 2003-2007.

4. Mutanen shiyyar Funtua sun zabi Lado a matsayin Sanata mai wakiltar kudancin Katsina a zaben 2007 karkashin inuwar PDP.

5. Yana matsayin Sanata ya nemi takarar gwamnan Katsina a inuwar CPC da aka rushe. Ya sha kaye hannun gwamna mai ci a wancan lokacin, Ibrahim Shema.

6. Katsinawa sun zargi Lado da sayar da yancinsa ta bayan fage a lokacin zaben gwamnan 2007, lamarin da har yau wasu ke sukarsa da shi.

7. PDP ta tsayar da Lado takarar gwamna a zaben 2019, amma ya sake shan kasa hannun gwamna Aminu Masari na jam'iyyar APC.

8. A yanzu, Garba Yakubu Lado na kokarin ganin ya zama gwamnan Katsina karƙashin PDP a zaben 18 ga watan Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel