Hukumar INEC Ta Dage Zaben Gwamnoni da Yan Majalisun Jihohi

Hukumar INEC Ta Dage Zaben Gwamnoni da Yan Majalisun Jihohi

  • INEC ta tabbatar da matsar da zaben gwamnoni da yan majalisar jihohi daga 11 zuwa 18 ga watan Maris, 2023
  • A wata sanarwa da yammacin Laraba, INEC ta ce ta ƙara mako ɗaya ne saboda saita na'urar BVAS sama da 176,000
  • Wannan lamari ya zo ne yayin da ya rage kwanaki uku kacal a fafata zaben ranar Asabar

Abuja - Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ɗage zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi wanda ta tsara gudanarwa ranar Asabar 11 ga watan Maris, 2023.

A wata sanarwa da INEC ta wallafa a Tuwita mai ɗauke da sa hannun Festus Okoye, kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan mutane, ta ce yanzu zaɓen ya koma Asabar 18 ga watan Maris.

Takardan sanarwa daga INEC.
Hukumar INEC Ta Dage Zaben Gwamnoni da Yan Majalisun Jihohi Hoto: INECNigeria
Asali: Twitter

Hukumar ta ce ta ɗauki matakin dage zaben biyo bayan hukuncin Kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa wanda ya ba ta damar fara sake saita na'urorin BVAS.

Kara karanta wannan

Magana ta Tabbata, INEC Ta Bada Uzurin Daga Zaben Jihohi Zuwa Mako Mai Zuwa

A cewar INEC, hukuncin da Kotun ta yanke yau Laraba ya zo a kurace kuma ya ba ta damar fara shirin sake saita BVAS domin tunkarar zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sakamakon haka, INEC ta ɗauki mataki mai wahala amma ya zama tilas na ɗaga zaben gwamnoni da mambobin majalisar jihohi, wanda a yanzu zai gudana ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023."
"Bisa haka, harkokin kamfe zasu ci gaba har zuwa tsakar daren ranar Alhamis, 16 ga watan Maris, watau awanni 24 gabanin sabuwar ranar gudanar da zaɓe."

- INEC.

Babban dalilin da ya sa INEC ta ɗage zabe

Sanarwan ta ƙara da cewa INEC ba ta ɗauki wannan matakin haka nan kawai ba sai don ya zama wajibi domin tabbatar da samun isasshen lokacin saita bayanan na'urorin BVAS sama da 176,000.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Farfesa Mahmood Da Kwamishinoni INEC Suna Ganawar Sirri Kan Zaben Gwamnoni

Hukumar ta ce bayan goge bayanan zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya zata saita na'urorin domin a yi amfani da su a zaben gwamnoni da yan majalisun jiha.

"Muna kara gode wa yan Najeriya da kawayen kasar nan bisa fahimtar mu yayin da muke kokarin ganin mun shawo kan komai kuma mu tsallake wannan lokaci mai cike da kalubale."

INEC Ta Soke Zabe a Mazabar Shugaban Masu Rinjaye, Ado Doguwa

A wani labarin kuma INEC ta ce za'a sake shirya zabe a mazabu 13 da ke yankin karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano

Baturen zaben yankin mazaɓar Doguwa/Tudun Wada ya ce zaben bai kammala ba sakamakon akwai rumfuna 13 da ake soke.

Ya bayyana sakamakon kuri'un da kowace jam'iyya ta sanu, amma tazarar ba ta da yawa tsskanin APC da NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel