Zababbun ‘Yan Majalisa Masu Neman Shugabanci a Majalisar Wakilai da Dattawa

Zababbun ‘Yan Majalisa Masu Neman Shugabanci a Majalisar Wakilai da Dattawa

  • Sani Musa, Barau Jibrin, Orji Uzor Kalu, Godswill Akpabio su na harin kujerar Ahmad Lawan
  • A majalisar wakilan tarayya, watakila a gwabza tsakanin Ahmed Idris Wase da su Muktar Betara
  • Babu mamaki Olubunmi Tunji-Ojo, Oluwole Oke da Olaide Akinremi su nemi mukamai masu tsoka

Abuja - Lissafi ya koma kan wanda zai zama shugaban majalisar wakilan tarayya bayan nasarorin da ‘yan takara suka samu a zaben 25 ga watan Fubrairu.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar Kudu maso yamma su na hangen kujerar mataimakin shugaban majalisa, hakan ya nuna shugabanci zai bar yankin.

Akwai wasu na kusa da Femi Gbajabiamila da suka nuna su na sha’awar bin sahunsa, amma har yanzu cikinsu babu wanda ya fito fili, ya bayyana aniyarsa.

Rahoton ya ce masu neman mukamai a majalisa ta goma sun hada Olubunmi Tunji-Ojo (APC/Ondo); Oluwole Oke (PDP/Osun); da Olaide Akinremi (AP/Oyo).

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar APC Ya Samu Gagarumar Goyon Baya a Zaben Shugabancin Majalisa

Za ayi wa Jam'iyya biyayya

Tunji-Ojo ya shaida cewa yana tare da jam’iyya a kan yankin da aka warewa kujerar shugaban majalisa, zuwa yanzu APC ba ta dauki matsaya a kan batun ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babajimi Benson wanda na hannun daman Gbajabiamila ne, kuma na kusa da Bola Tinubu, ya ce sai yadda jam’iyya ta ce a kan kason mukaman majalisar.

Zababbun ‘Yan Majalisa
Hon. Ahmed Idris Wase Hoto: @ahmad.ganga.545
Asali: Facebook

Da wahala da Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila su rike kujerunsu a dalilin nasarar Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Shirin 'Yan majalisar wakilai

Zuwa yanzu ‘yan majalisar da suke hangen shugabanci sun kunshi Ahmed Idris Wase da Mukhtar Aliyu Betara da suka samu tazarce a APC mai rinjaye.

Akwai Alhassan Ado Doguwa a lissafin, amma magana ta canza bayan INEC ta soke nasararsa, sannan ana shari’a da shi a kotu a kan zargin kisan kai a Kano.

Kara karanta wannan

"An Hada-Kai da INEC, Za a Murde Zaben Gwamna a Jihar Adamawa" Inji Jam’iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta fahimci a Arewa maso yamma akwai Aminu Jaji, daga Arewa ta tsakiya akwai Ahmad Wase, sai Mukhtar Batera daga Arewa maso gabas.

...Majalisar Dattawa

A majalisar dattawa, Sanatocin da suke neman manyan mukamai a 2023 sun hada da Barau Jibrin, Orji Uzor Kalu, Godswill Akpabio da Muhammad Sani Musa.

Wata majiya ta ce Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu yana goyon bayan Sanatan gabashin Neja, Sani Musa ya karbi shugabancin majalisar dattawa.

Mata a Majalisar Dattawa

Rahoto ya zo cewa a cikin zababbun Sanatocin Najeriya, Ireti Heebah Kingibe da Banigo I. Harry ne kurum matan da za su je majalisar dattawa a 2023.

Banigo I. Harry ta yi Kwamishinar ma'aikatar lafiya da SGF kafin zama Mataimakiyar Gwamna. Kingibe za ta zama mace ta biyu da ta zama Sanatar Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel