‘Dan Majalisar APC Ya Samu Gagarumar Goyon Baya a Zaben Shugabancin Majalisa

‘Dan Majalisar APC Ya Samu Gagarumar Goyon Baya a Zaben Shugabancin Majalisa

  • Rotimi Akeredolu da Yahaya Bello za su goyi bayan takarar Ahmed Idris Wase a Majalisar Wakilai
  • Hon. Ahmed Idris Wase ya ci burin zama Shugaban majalisar wakilan tarayya a zaben da za a shirya
  • Gwamnonin su na cikin masu ganin cancantar Mataimakin shugaban majalisar ya gaji Femi Gbajabiamila

Abuja - Gwamnonin Ondo da Kogi, Rotimi Akeredolu da Yahaya Bello sun nuna goyon bayansu ga Arewa maso tsakiya su fito da shugaban majalisa.

Vanguard ta ce Gwamna Rotimi Akeredolu da takwaransa Yahaya Bello sun bayyana matsayarsu bayan zama da Hon. Ahmed Idris Wase a makon nan.

Gwamnonin biyu sun shaidawa Duniya za su goyi bayan sabon shugaban majalisar wakilan tarayya ya fito daga yankin Arewa maso tsakiya a 2023.

Hakan ya fito ne bayan mataimakin shugaban majalisa kuma ‘dan takara a bana, Ahmed Idris Wase ya kai wa kowanensu ziyarar neman goyon baya.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta Kunshe Biliyoyin Kudi Wajen Saida Fam Ga Masu Sha’awar Takara

Wase yana ta kamfe

Hon. Wase ya ziyarci Gwamnan jihar Kogi a gidansa da ke garin Abuja a ranar Litinin, kafin nan kuma ya yi zama da Gwamna Rotimi Akeredolu a Akure.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Dan majalisar ya yi zama da Gwamnan na jihar Ondo a gidan gwamnati a karshen makon nan. Jaridar Leadership ta fitar da makamancin wannan rahoto.

Ahmed Idris Wase
Hon. Ahmed Idris Wase a Majalisa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake jawabi, an rahoto Yahaya Bello yana cewa nauyi ne a kan shi ya marawa yankinsa na Arewa ta tsakiya baya wajen samun shugabancin majalisa.

Shi kuwa Mai girma Rotimi Akeredolu ya fito karara yana yabon ‘dan majalisar na Filato, ya ce yana cikin kusoshin da jam’iyyar APC take takama da su.

Gwamnan na Ondo yake cewa yana mamaki idan mutane su ka tambaye shi ko ya san Hon. Wase.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikici Ya Tsananta, Gwamna Wike Ya Maida Martani Mai Zafi Kan Dakatar da Shugaban PDP

Baya ga sanayya da ke tsakaninsu, Akeredolu ya yi wa ‘dan takaran shaida a matsayin wanda yake yi wa jam’iyya biyya kuma ya cancanta da mukami.

Meya faru da APC a Katsina

A zaben shugaban kasa da aka yi, Atiku Abubakar ya samu kuri’u 489,045 yayin da Bola Tinubu da ya tsaya takara a APC ya kare da 482,283 a Jihar Katsina.

Amma a zaben Gwamnan Katsina, sai Jam’iyyar APC ta ba PDP rata mai ‘dan karen yawa. An rahoto Dr. Dikko Umaru-Radda yana bayanin abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel