Dubunnan Magoya Bayan PDP Sun Koma Bayan Ɗan Takarar Gwamnan APC a Jihar Oyo

Dubunnan Magoya Bayan PDP Sun Koma Bayan Ɗan Takarar Gwamnan APC a Jihar Oyo

  • Ana dab da a fara zaɓen gwamna, dubun dubatar magoya bayan jam'iyyar PDP sun koma bayan ɗan takarar gwamnan APC a jihar Oyo
  • Wannan dai ba ƙaramin koma baya bane ga gwamnan jihar wanda yake neman komawa kan kujerar mulki a karo na biyu
  • Magoya bayan na jam'iyyar PDP sun bayyana cewa zaɓen gwamnan jihar na da matuƙar muhimmanci don haka mutanen jihar su shirya yadda yakamata

Jihar Oyo- Kusan magoya bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mutum 190,000 ne suka koma bayan ɗan takarar gwamnan All Progressives Congress (APC), Teslim Folarin.

Dubun dubatar magoya bayan na jam'iyyar PDP, sun bayyana cewa suna tare da ɗan takarar gwamnan APC a zaɓen gwamnan da za ayi na ranar 11 ha watan Maris 2023. Rahoton The Punch

Folarin
Dubunnan Magoya Bayan PDP Sun Koma Bayan Ɗan Takarar Gwamnan APC a Jihar Oyo Hoto: The Punch
Asali: UGC

Magoya bayan waɗanda ke da ƙungiyar su mai suna PDP Vanguard, sun bayyana hakan ne a shafin su na Twitter @pdpvanguard, a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ana Gobe Zaɓe, Sanatan APC Ya Samu Tagomashi, Ƴan Takara 8 Sun Janye Masa Takara

Sanarwar na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yana da matuƙar amfani duk wanda ya cancanci kaɗa ƙuri'a a jihar Oyo ya sauke haƙƙin sa na yin zaɓe."
“Hakan yana da matuƙar muhimmanci, domin kowace ƙuri'a tana da amfani kuma zata yi tasiri a zaɓen dake tafe."
"Folarin shine mafita!”

A halin da ake ciki ɓangaren ɗan takarar gwamnan APC na jihar Oyo, yayi maraba da wannan goyon baya da ƙungiyar ta basu.

A wata sanarwa da hadimin ɗan takarar na ɓangaren watsa labarai, Yekeen Olaniyi, ya fitar a ranar Alhamis, ya nuna jindaɗin sa kan samun wannan tagomashin da ɗan takarar ya samu.

Ya kuma yi kira ga sauran jam'iyyun adawa da su bi sahun PDP Vanguard ta hanyar mara masa baya domin ceto jihar daga mulkin gwamna Seyi Makinde na jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Zasu Taka Muhimmiyar Rawa a Zaɓen Shugaban Ƙasa

A kalaman sa:

“Abun kunya ne yadda tsaro a jihar Oyo ya taɓarɓare daga kyawun da aka san shi da shi tun lokacin "Operation Burst” inda ya koma abin cizon yatsa a yanzu,
"Ta yadda mutanen jihar Oyo yanzu sun koma rayuwa cikin ɗar-ɗar da tashin hankali."

Babban Jigon PDP Ya Yi Fatali da Okowa, Ya Koma APC Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

A wani rahoton, wani jigo a jam'iyyar PDP ya koma bayan Tinubu, yayi fatali da tafiyar Atiku Abubakar.

Lamarin na zuwa ne bayan Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel