Zaben Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa Abu Ne Mai Kyau, Gwamna Masari

Zaben Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa Abu Ne Mai Kyau, Gwamna Masari

  • Gwamnan Katsina ya nuna farin ciki da nasarar Bola Tinubu na zama zababben shugaban ƙasa a Najeriya
  • Masari ya ce zaben tsohon gwamnan Legas shi ne abinda ya dace kuma Allah ya nuna karfin mulkinsa
  • Ya kuma sake kira ga Katsinawa da su fito kwansu da kwarkwata su zabi Dikko Radda ranar 11 ga watan Maris, 2023

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ranar Laraba, ya nuna farin cikinsa da nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na zama zababben shugaban ƙasa a Najeriya.

Gwamna Masari ya ayyana nasarar ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu, da zaɓi nagari wanda ya dace da Najeriya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu da tawagarsa suna murnar lashe zabe Hoto: ABAT
Asali: UGC

Gwamna Masari ya yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa 2023.

Kara karanta wannan

Na Hannun Dama Ya Ba Tinubu Shawara Ya Jawo Kwankwaso da Peter Obi a Gwamnati

Ya ƙara da cewa zababben shugaban kasa mutum ne mai basira, hangen nesa, kuma mutum ne da yake maraba da kowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa ta gano cewa gwamnan Katsina da wasu daga cikin mambobin majalisar zartaswansa sun zauna wuri guda a gidan gwamnati suna kallon yadda INEC ke tattara sakamako har zuwa karshe.

Yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan Tinubu ya ci zaɓe, Masari ya yaba da kwazon INEC, hukumomin tsaro da ɗauƙacin 'yan Najeriya kan yadda zaɓen ya gudana.

A kalamansa, Aminu Masari ya ce:

"Allah ya wanke ni sarai da sauran yan Najeriya ta hanyar kunyata waɗanda su ke tantamar INEC ba zata iya aiwatar da sahihin zaɓe ba. Mun yi nasara saboda mun fito kwanmu da kwarkwata tare da magoya baya mun zabi Tinubu."
"Ba zan gajiya ba ina kira ga magoya baya su fito kwansu da kwarkwata su zabi Dakta Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama magaji na a matsayin gwamnan Katsina a zaben da ke tafe ranar 11 ga watan Maris, 2023."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: INEC Ta Bayyana Wanda Ya Samu Nasara a Karamar Hukumar Gwamna Wike

"Kwankwaso Gwarzo Ne" NNPP Ta Maida Martani Kan Nasarar Tinubu

A wani labarin kuma Jigon jam'iyyar NNPP ya bayyana yadda INEC da wasu jam'iyyu uku suka fito da makamai don yaƙar Kwankwaso

Buba Galadima, tsohon na hannun daman shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce zaben ranar Asabar ya ƙara nuna cewa Kwankwaso gwarzo ne.

A cewarsa, kuri'un da INEC ta ayyana a matsayin wanda NNPP ta samu a baki ɗaya Najeriya ba su kai adadin wanda suka samu a Kano kaɗai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel