Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Cikakken Jerin Jihohin Da Bola Tinubu Na APC Ya Lashe
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta kammala tattara sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
An tattara sakamakon zaben ne a dakin taro na kasa da kasa, ICC, da ke birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Zaben shugaban kasa na 2023: Tattara sakamakon zabe a Abuja
An tattara sakamakon zabe daga jihohi 36 na kasa da birnin tarayya Abuja a mataki na kasa a Abuja. Su ne:
- Jihar Ekiti
- Jihar Kwara
- Jihar Osun
- Jihar Ondo
- Jihar Ogun
- Jihar Oyo
- Jihar Yobe
- Jihar Enugu
- Jihar Lagos
- Jihar Gombe
- Jihar Jigawa
- Jihar Adamawa
- Jihar Katsina
- Jihar Nasarawa
- Jihar Niger
- Jihar Benue
- FCT, Abuja
- Jihar Akwa Ibom
- Jihar Edo
- Jihar Abia
- Jihar Kogi
- Jihar Bauchi
- Jihar Plateau
- Jihar Bayelsa
- Jihar Kaduna
- Jihar Kebbi
- Jihar Zamfara
- Jihar Kano
- Jihar Sokoto
- Jihar Cross River
- Jihar Delta
- Jihar Ebonyi
- Jihar Anambra
- Jihar Taraba
- Jihar Borno
- Jihar Rivers
- Jihar Imo
Daga cikin jihohi 36 da Abuja da aka lissafa a sama, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya lashe 12 yayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, shi kuma ya lashe 12.
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, LP, ya lashe 12 yayin da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya lashe jiha daya tak.
Zaben shugaban kasa na 2023: Jihohi nawa Tinubu ya lashe?
- Jihar Ekiti
- Jihar Ondo
- Jihar Kwara
- Jihar Ogun
- Jihar Oyo
- Jihar Jigawa
- Jihar Borno
- Jihar Rivers
- Jihar Kogi
- Jihar Zamfara
- Jihar Niger
- Jihar Benue
Asali: Legit.ng