‘Dan Siyasar da Ya Samu Takara Yana Hannun ‘Yan Bindiga Ya Doke APC a Kaduna

‘Dan Siyasar da Ya Samu Takara Yana Hannun ‘Yan Bindiga Ya Doke APC a Kaduna

  • Sulaiman Abdu Kwari ya rasa takarar tazarcensa a wajen Khalid Ibrahim-Mustapha a Kaduna
  • A Majalisar wakilai, wani ‘dan PDP, Sadiq Ango Abdullahi ya doke Hon. Garba Datti Muhammad
  • Jam’iyyar PDP mai hamayya a jihar ta raba wasu ‘yan APC da kujerun majalisa a zaben nan na bana

Kaduna - Hukumar zabe mai zaman kan ta watau INEC, ta sanar da Khalid Ibrahim-Mustapha a matsayin wanda zai zama Sanatan Arewacin Kaduna.

Premium Times ta ce Khalid Ibrahim-Mustapha wanda aka fi sani da Khalid Soba ya doke Sulaiman Abdu Kwari, ya hana sa komawa majalisar dattawa.

Farfesa Saleh Ado na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya sanar da sakamakon zaben a ranar Litinin.

Kamar yadda Farfesa Saleh Ado ya shaida dazu, jam’iyyun siyasa 12 suka shiga wannan takara da Khalid-Mustapha ya samu galaba da kuri’u 250, 026.

Kara karanta wannan

APC ta Rasa Duka Sanatocinta a Jihar Arewa, An Yi Sukuwa a Kan Jam’iyya Mai-Ci

Farfesan ya ce wanda ya zo na biyu, Kwari Suleiman Abdu na jam’yyar APC yana da kuri’u 190,008, sannan NNPP da LP suka kare da 28, 511 da 28, 418.

Rahoton ya ce Ahmed Wakili, Abdullahi Suleiman da Hassan Muktari na PRP, ADC da ZLP sun sha kashi, don haka aka tabbatar da nasarar PDP a zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kaduna
Gwamnan Kaduna da Muhammad Sani Dattijo Hoto: @dattijo
Asali: Facebook

Dattijo ba zai je Majalisa ba

A wani labarin a gidajen rediyo, Lawal Adamu Usman wanda jama’a suka fi sani da Mista LA, ya doke Muhammad Sani Dattijo a yankin Kaduna ta tsakiya.

‘Dan takaran na PDP ya doke tsohon Kwamishinan Nasir El-Rufai wanda ya tsaya takara a APC. Matashin zai canji Uba Sani a majalisar dattawan kasar.

Lokacin Sadiq Ango Abdullahi ya yi

Legit.ng Hausa ta samu labari Sadiq Ango Abdullahi ya yi galaba a PDP a kan Garba Datti Muhammad mai wakiltar mazabar Sabon Gari a majalisa tun 2007.

Kara karanta wannan

Kanin Tsohon Shugaban Kasa ‘Yar’adua Zai Zama Sanatan Katsina a Majalisar Dattawa

Tuni Hon. Garba Datti ya rungumi kaddara, ya kira Sadiq Ango, ya yi masa murnar lashe zabe, kuma ya yi kira ga magoya baya da su karbi sakamakon.

Sauran kujerun majalisar wakilan tarayya da PDP ta karbe daga hannun ‘yan APC a jihar Kaduna sun hada da na Makarfi/Kudan, Ikara/Kubau da Soba.

Canza takardun kudi

A baya kun ji labari wasu Gwamnoni sun fito su na sukar tsarin canza kudi, gwamnati ta ce hakan zai yi maganin barayin da suke shirin magudi.

Abubakar Malami SAN ya nuna makomar irinsu Nasir El-Rufai da Abdullahi Ganduje a kan zargin cin amanar kasa ta na wajen Jami’a tsaro da ke bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel