Zaben 2023: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Gayara Najeriya, Gwamna Ben Ayade

Zaben 2023: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Gayara Najeriya, Gwamna Ben Ayade

  • Gwamnan jihar Kuros Riba ya bayyana ra'ayinsa game da wanda zai iya gyara Najeriya bayan shugaba Buhari
  • Farfesa Ben Ayade yace matukar Bola Tinubu ya iya gyara Legas to ba abinda zai hana shi tsamo Najeriya daga kakanikayi
  • Dan takarar gwamnan APC a jihar ya sha alwashin dora wa daga inda gwamnatin Ayade ta tsaya

Cross River - Gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ne kaɗai ke da gogewar jan ragamar Najeriya zuwa gaba.

Gwamna Ayade, mai neman zama Sanatan Kuros Riba ta arewa a inuwar APC, ya yi wannan furucin ne a garin Ogoja, cibiyar siyasar arewacin jihar yayin kamfe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Zaben 2023: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Gayara Najeriya, Gwamna Ben Ayade Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Farfesa Ayade yace Tinubu zai ɗauki ayyukan raya ƙasa da ci gaban jihar Kuros Riba da matukar muhimmanci idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Atiku Ko Obi? Babban Jigon APC Kuma Ɗan Kwamitin Amintattu Ya Aje Tinubu, Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a 2023

"Idan Tinubu ya iya gyara jihar Legas, alama ce ta zai iya gyara Najeriya," a cewar gwamna Ayade, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake jawabi a wurin ralin, wanda ɗaruruwan mambobin PDP suka sauya sheka zuwa APC, Gwamna Ayade ya roki mutanen yankin su zabi APC sak don saka aƙherin ayyukan da ta masu a Ogoja.

Ya jaddada cewa gaskiya, adalci, daidaito da kwarewar sanin makamar aiki zasu samu gindin zama idan Tinubu da Otu suka zama shugaban ƙasa da gwamna a zabe mai zuwa.

Zamu dora daga inda Ayade ya tsaya - Otu

A wurin Ralin, dan takarar gwamnan APC a jihar Kuros Riba, Sanata Bassey Otu, ya yi kira ga mutane su zabe shi tare da mataimakinsa, Honorabul Peter Odey, wanda haifaffen yankin ne.

Sanata Otu ya yi alƙawarin cewa zai dora daga inda gwamnatin Ayade ta tsaya. Ya kara da bayanin cewa Ayade zai bar tubali mai kyau a bangaren masana'antu kuma idan ya gaje shi zai ƙarisa.

Kara karanta wannan

2023: Wani Gwamnan APC Ya Janye Daga Kamfen Bola Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

A wani labarin kuma Babban Jigon APC Kuma Ɗan Kwamitin Amintattu Ya Aje Tinubu, Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a 2023

Babban mai faɗa aji a siyasar jihar Abiya kuma mamban kwamitin amintattun APC, Prince Apugo, ya ayyana goyon baya ga yan takarar Labour Party.

Ya ce Peter Obi na da kwarewar da ake bukata daga shugaban ƙasa na gaba domin ceto ƙasa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel