Yadda Bola Tinubu Ya Kawo Karshen Mummunan Rikicin Jam’iyyar APC Cikin Ruwan Sanyi

Yadda Bola Tinubu Ya Kawo Karshen Mummunan Rikicin Jam’iyyar APC Cikin Ruwan Sanyi

  • An yi ta zuwa kotu tsakanin Sanata John Owan Enoh da Sanata Bassey Otu kan neman tikitin APC a 2023
  • Jam’iyyar APC ta tsaida Otu a matsayin ‘dan takaran Gwamnan Kuros Ribas, Enoh bai yarda da wannan ba
  • Yanzu an yi watsi da karar da ke gaban koli a sakamakon Bola Tinubu ya fito fili ya ba Sanata Enoh hakuri

Cross River - Asiwaju Bola Tinubu ya yi abin da kusan ya gagari kowa a jam’iyyar APC mai-ci, ya sasanta bangarorin da ke rikici a jihar Kuros Riba.

A dalilin sa bakin da ‘dan takaran shugaban kasan na 2023 ya yi, Sanata John Owan Enoh ya hakura da zuwa kotu. Leadership ta fitar da wannan rahoto.

Asiwaju Bola Tinubu ya lallashi John Owan, hakan kuma ya yi tasiri domin tsohon Sanatan ya jinginar da shari’arsa na ganin ya samu takarar Gwamna.

Kara karanta wannan

Asalin Abin da Ya Sa Gwamnonin PDP Suka Hadu da Tawagar Tinubu Ta Bayyana

John Owan Enoh ya yi niyyar ya tafi kotun koli domin ya yi shari’a da ‘dan takaran Gwamnan da jam’iyyar APC ta tsaida a zaben 2023 a jihar Kuros Riba.

An yi ta shiga kotu babu nasara

Hakan na zuwa ne bayan an yi ta gwabzawa da shi a gaban kotun tarayya mai zama a Kuros Riba da kuma babban kotun daukaka kara da ke garin Kalaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi a garin Abuja a makon nan, Daily Trust ta rahoto tsohon ‘dan majalisar ya ce ba zai cigaba da kalubalantar APC da ‘dan takaransu ba.

'Dan takaran APC
'Dan takaran APC, Bola Tinubu a taro Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Baya ga janye kara da Sanata Enoh ya yi, ya yi alkawarin zai taimakawa jam’iyyarsa ta APC mai mulkin Najeriya wajen ganin tayi galaba a zaben na 2023.

The Guardian ta ce ‘dan siyasar ya yi alwashin zai yi wannan ne albarkacin sa bakin da tsohon gwamnan jihar Legas yayi a rikicinsa da Sanata Bassey Otu.

Kara karanta wannan

Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36

Jawabin Sanata John Owan Enoh

"Taron da aka yi da ‘dan takaran shugaban kasar jam’iyyarmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yayyafa mani ruwa a zuciyata.
Kuma ya kawo karshen kokarin da nake yi wajen neman ganin an yi mani adalci.
Fitowa fili da ‘dan takaran shugaban kasa kuma jagora a jam’iyyarmu ya yi, ya nuna kwantar da kai, ba zan iya yin watsi da shi ba.
Dole na zauna da dangi na da dinbin magoya bayana da ke jihar bayan wannan taro. Ina mai kawo karshen shari’ar, zan taimaki APC."

- John Owan Enoh

Rokon Magoya bayan Tinubu

An samu rahoto cewa Tinubu/Shettima Network (TSN) 2023 ta na ganin duk mai adawa da Bola Ahmed Tinubu yana asarar dukiya da lokacinsa ne.

Shugaban TSN 2023 a Najeriya, Dr. Kailani Muhammad ya nemi Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi su shiga jirgin APC a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Sa Ranar da APC, Tinubu Za Su San Makomarsu a Kan Takara a Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel