Asalin Abin da Ya Sa Gwamnonin PDP Suka Hadu da Tawagar Tinubu Ta Bayyana

Asalin Abin da Ya Sa Gwamnonin PDP Suka Hadu da Tawagar Tinubu Ta Bayyana

  • An samu karin bayanin abin da ya sa Gwamnonin PDP da ke cikin G5 suka zauna da su Bola Tinubu
  • Gwamnonin jihohin sun rufe duk wata kofar yin sulhu da Atiku Abubakar mai neman mulkin Najeriya
  • ‘Yan G5 sun fara duba yiwuwar marawa wani daga cikin ‘yan takara baya a zaben shugaban kasan 2023

United Kingdom - Gwamnonin da ake rigima da su a jam’iyyar PDP sun yi zama na musamman da kusoshin jam’iyyar APC a birnin Landan a kasar Ingila.

Rahoton The Nation ya nuna Nyesom Wike, Seyi Makinde, Okezie Ikpeazu, Ifeanyi Ugwuanyi da Samuel Ortom sun ki yarda ayi wannan zaman sulhu a PDP.

Wani a cikin Gwamnonin da ake rigima da su a PDP ya shaida cewa taronsu na Landan yana cikin kokarinsu na tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36

Gwamnan ya ce nan da watan Junairu za su sanar da Duniya matsayar da suka dauka, ya ce babu dalilin garaje, domin za a san wa za su marawa baya a 2023.

Babu sulhu a Jam'iyyar PDP

Gwamna Nyesom Wike da mutanensa da ‘yan kungiyar Integrity Group ba su goyon bayan takaran da Atiku Abubakar yake yi a jam’iyyar PDP a zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta ce ‘yan kungiyar na G5 sun rufe kofar zama da Atiku Abubakar ne domin ya ki yarda da bukatarsu na sauke shugaban PDP, Dr. Iyorchia Ayu.

Gwamnonin PDP
Gwamnonin Ribas da na Abia Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Baya ga haka, cire Seyi Makinde da aka yi a matsayin shugaban yakin neman zaben PDP a yankin Kudu maso yammacin Najeriya ya fusata gwamnonin G5.

Wani mataki 'Yan G5 za su dauka?

Ana tunanin matsayar da Gwamnonin suka dauka shi ne ba za su marawa wani ‘dan takara baya a zaben shugaban kasa ba, za su cire hannunsu a lamarin.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Gwamna da Wasu Kusoshin APC Sama da 500 Sun Koma PDP, Abokin Gamin Atiku Ya Magantu

Amma a zaben ‘yan majalisar tarayya da sauran na jihohi, gwamnonin za su goyi bayan wadanda jam’iyyar PDP ta tsaida a matsayin ‘yan takara a badi.

Rahoton ya ce Janar Aliyu Gusau mai ritaya yana ta kokarin ya zauna da gwamnonin G5 domin ayi sulhu, amma sun ki ba shi dama, suna zargin shi da son-kai.

Zabin da ‘Yan G5 suke da shi su ne:

1. Su yi karam-bani, su goyi bayan Bola Tinubu ko Peter Obi.

2. Su ba Bola Tinubu ko Peter Obi gudumuwa, su taya su kamfe.

3. A bar kowane Gwamna ya dauki zabin da ya dace da jiharsa.

4. Su ki yi wa Atiku Abubakar kamfe, su bar mutanensu da zabi.

5. Su yi gum da bakinsu, su boye shirin da suke yi sai daf da zabe.

PDP za ta hukunta 'Yan G5

An ji labari Jam’iyyar PDP ta na kokarin koyawa Gwamnoninta Nyesom Wike, Okezie Ikpeazu, Samuel Ortom, Seyi Makinde da Ifeanyi Ugwuanyi darasi.

Kara karanta wannan

Sabon salo: 'Ya'yan Buhari za su taya matasan Najeriya tallata Tinubu da APC gabanin 2023

A tsari da dokar PDP, Jam’iyya tana da wuka da nama da za ta iya ladabtar da duk wanda yake shirya zagon-kasa da makarkashiya ga 'dan takaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel