Zaben 2023: Abin Kunya Ne Buhari Ya Mika Mulki Ga Yan Adawa, In Ji Abdullahi Adamu

Zaben 2023: Abin Kunya Ne Buhari Ya Mika Mulki Ga Yan Adawa, In Ji Abdullahi Adamu

  • Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ce zai zama abin kunya Shugaba Buhari ya mika mulki ga yan adawa
  • Adamu ya bayyana cewa duk wani mahaluki da ke tunanin ya fi Buhari son ganin APC ta ci zaben 2023 karya ya ke yi
  • Jigon na APC ya kuma karyata cewa Shugaba Buhari yana janye kansa daga kamfen din Bola Tinubu, yana mai cewa yana da aiki a matsayin shugaban kasa a gabansa

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Adamu ya ce zai zama abin kunya Shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulki ga jam'iyyar hamayya a 2023, Daily Trust ta rahoto.

A hirar da ya yi da BBC Hausa, shugaban jam'iyyar na kasa ya ce Buhari ya fi kowa son jam'iyyar APC ta ci zabe.

Kara karanta wannan

Wadanda Ke Zagaye da Buhari Duk an Nada su Ba Don Cancanta ba, Jigon APC

Abdullahi Adamu
Abin Kunya Ne Buhari Ya Mika Mulki Ga Yan Adawa, In Ji Adamu. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adamu ya yi watsi da zargin cewa Buhari na nesanta kansa ga yi wa Tinubu kamfe

Da ya ke watsi da zargin da ake yi na cewa Shugaba Buhari na janyewa daga yi wa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, kamfen, Adamu ya ce ba daidai bane ya bar aikinsa a matsayin shugaban kasa saboda zabe.

Ya ce:

"Abubuwa na tafiya yadda muke so, muna gode wa Allah, kowa cikin tafiyar mu na ganin Allah na tare da mu. Munyi imani da nasara, dukkan sauran jam'iyyun sun san muna gaba da su."

Kan zargin cewa Buhari ya janye daga yi wa jam'iyyarsa kamfen, Adamu ya ce ba gaskiya bane.

Ya kara da cewa:

"Duk wanda ya fada maka cewa ya fi Buhari son ganin jam'iyyar APC ta yi nasara karya ya ke. Dalili na shine abin kunya ne ga Shugaban kasa ya mika mulki ga jam'iyyar siyasar da ba nashi bane.

Kara karanta wannan

Bana son rigima: Buhari ya fadi abu 1 da zai yi bayan sauka daga mulki a 2023

"Abin da mutane ba su lura cewa Muhammadu Buhari shugaban kasa ne kuma akwai rantsuwa da ya yi cewa kowane dan Najeriya nasa ne. Don haka dole ya yi taka tsantsan idan ba haka ba yan adawa za su ce APC ya ke yi wa aiki a maimakon Najeriya."

Zaben 2023: Mahmoud Maijama'a ya fita daga APC ya koma PDP

A wani rahoton, Alhaji Mahmoud Maijama'a, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Bauchi ya fita daga APC ya koma PDP.

Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ne ya tarbi Maijama'a da dimbin magoya bayansa da suka sauya shekarar tare, Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel