2023: Dan Takarar Gwamnan APC A Bauchi, Maijama’a Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

2023: Dan Takarar Gwamnan APC A Bauchi, Maijama’a Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a kasar ta yi babban kamu a jihar Bauchi gabannin babban zaben 2023
  • Alhaji Mahmoud Maijama’a wanda ya nemi takarar gwamna a jam'iyyar APC mai mulki ya sauya sheka zuwa PDP
  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya tarbi Maijama'a da tarin magoya bayansa a gidan gwamnati

Bauchi - Dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi, Alhaji Mahmoud Maijama’a, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Maijama’a wanda ya koma PDP tare da dandazon magoya bayansa ya samu tarba daga Gwamna Bala Mohammed a gidan gwamnati da ke Bauchi, jaridar Leadership ta rahoto.

APC da PDP
2023: Dan Takarar Gwamnan APC A Bauchi, Maijama’a Ya Sauya Sheka Zuwa PDP Hoto: PM News
Asali: UGC

Gwamna Mohammed ya ce har gobe PDP ce babbar jam'iyyar siyasa a nahiyar Afrika wacce ke goyon bayan yan Najeriya a dukkan lokaci baya ga tunani, girma da hakuri da take da shi.

Kara karanta wannan

Shinkenan ta takewa Tinubu, 'yan jiharsa su bayyana dan takarar da za su zaba ba shi ba

Ya ce gwamnatinsa ta yiwa al'umma shugabanci nagari tare da shayar da su romon damokradiyya baya ga manufofin da ta gabatar don inganta rayuwar mutane da sauya kallon da ake yiwa jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da yake yiwa masu sauya shekar maraba da zuwa PDP, gwamnan ya yi kira garesu da su marawa kudirin gwamnatinsa na tallafawa matasa da mata a fadin jihar baya.

Ya ce hakan na daga cikin kokarin da suke yi don bunkasa tattalin arziki da zamantakewa a jihar Bauchi.

A nashi bangaren, Maijama'a ya yi alkawarin aiki don ci gaban jam'iyyar a babban zaben 2023.

Ya yi alkawarin yin biyayya ga shugabancin PDP mai ci a jihar, yama mai cewa dukkanin magoya bayansa za su zamo 'ya'yan jam'iyya masu bin doka.

An Yi Ca Kan Wani Dan Takarar Shugaban Kasa Kan Wani Takalmi da Ya Sanya a Wurin Kamfe

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dakta Aliyu Tilde, Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi Yayi Murabus, Ya Sanar da Dalili

A wani labari na daban, mun ji cewa jama'a sun yi ta cece-kuce bayan bayyanar wasu takalma da dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi ya saka zuwa wajen kamfen dinsa a jihar Imo.

Takalman dai sun yi fata-fata da kura don haka mutane suka ce lallai shine yafi dacewa da Najeriya domin a cewarsa hakan ya tabbatar da shi mutum ne mai saukin kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel