‘Yan Sanda Sun Kama Yaro Mai Shekaru 16 kan Zagin Gwamna Buni, Za a Kaishi Kotu

‘Yan Sanda Sun Kama Yaro Mai Shekaru 16 kan Zagin Gwamna Buni, Za a Kaishi Kotu

  • ‘Yan sanda a jihar Yobe sun kama yaro mai shekaru 16 mai suna Umar Garba Isa kan zarginsa da zagin Gwamna Mai Mala Buni a soshiyal midiya
  • Mahaifin yaron mai suna Garba Isa mai sana’ar wanki da guga, ya roki Gwamnan da ‘yan sandan da su saki ‘dansa saboda tausayi kuma yafe masa
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya amsa cewa Umar yana hannunsu kuma za a mika shi kotu bayan kammala bincike don dole a tsaftace al’umma

Yobe - Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta cafke yaro mai shekaru 16 kan zarginsa da zagin Gwamna Mai Mala Buni na jihar a soshiyal midiya.

Gwamna Buni
‘Yan Sanda Sun Kama Yaro Mai Shekaru 16 kan Zagin Gwamna Buni, Za a Kaishi Kotu. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Duk da an kama yaron tun ranar 11 ga watan Disamban 2022, sai a ranar Litinin din nan labarin ya fito bayan mahaifin yaron mai suna Garba Isa yayi kira ga hukumomin ‘yan sanda da su saki ‘dansa.

Kara karanta wannan

Alhamdulillahi: 'Yan sanda sun kama wasu tsagerun masu garkuwa da mutane

Channels TV ta tattaro cewa an kama yaron a Nguru kuma daga bisani aka mayar da shi hannun rundunar ‘yan sandan dake Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

A yayin zantawa da Channels TV ta waya, Isa ya kushe dabi’ar ‘dansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai wanki da gugan yayi kira ga gwamnan da kwamishinan ‘yan sanda, Garba Haruna kan su saki ‘dansa saboda tausayi.

“Nayi nadamar abinda ‘dana yayi. Ni ba kowa bane, mai wanki da guga ne kuma abinda Umar yayi ba daidai bane.
“Ina kira ga Gwamna Mai Mala Buni da kwamishinan ‘yan sanda da su yafewa ‘dana kuma su sake shi.”

- Yace.

Dole mu tsaftace al’umma, Kwamishinan ‘Yan Sanda

A yayin da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan, ya amsa cewa wanda ake zargin yana hannunsu kuma yace ana kammala bincike za a mika shi gaban kotu.

Kara karanta wannan

Ta bare: Saura kiris biki ango ya gano budurwarsa na da 'ya'ya 2, ya dauki tsattsauran mataki

“Idan mun kammala bincike, za mu kai shi kotu. Jama’a na amfani da soshiyal midiya wurin zagi da bata sunan jama’a, ya dace a tsaftace al’umma.”

- kwamishinan ‘yan sandan yace.

“Ba zai yuwu a dinga amfani da soshiyal midiya ana wallafa kowanne irin shirme ba. Akwai doka da oda a Najeriya kuma duk wanda ya keta hakkin wani, dole ne a ladabtar da shi.”

- Ya kara da cewa.

Ku yafewa ‘danmu: Iyayen Dalibin da ya zagi Aisha Buhari

A wani labari na daban, iyaye dalibin jami’ar tarayya ta Jigawa, Aminu Muhammad, wanda ya zolayi Aisha Buhari a Twitter, sun roki a yafe masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel