Abdussamad Bua na Hamshakin Mai Arziki na 4 a Afrika, Dangote na ta Tafka Asara

Abdussamad Bua na Hamshakin Mai Arziki na 4 a Afrika, Dangote na ta Tafka Asara

  • Abdulsamad Rabiu ya shillara cikin jerin wadanda suka fi kowa kudi a Afirka yayin da arzkin sauran yayi kasa
  • Forbes ta ruwaito yadda a halin yanzu Abdulsamad ya zama mutum na hudu da yafi kowa arzki a Afirka, mataki daya sama da yadda ya fara a 2022
  • Hakan ya faru ne da Dangote da sauran biloniyoyi sukayi asarar sama da N3 triliyan a watanni uku da suka shude

Abdulsamad Rabiu, shugaban kamfani siminti na BUA ya haura zuwa mataki na hudu a jerin sunayen masu kudin Afirka wanda a yanzu ya kere biloniyan nan da Misira, Nassef Sawiris.

Kamar yadda Forbes ta ruwaito, Rabiu ya hada sama da $1.1 biliyan a shekarar 2022, wanda a yanzu yake da jimillar arzikin mai kimar $8.1 biliyan, samar da $7 biliyan yayin da shekarar ta fara.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaban Kasan South Sudan Yana Fitsari A Wando Ana Tsakiyar Taro

Kamfanin simintin BUA
Abdussamad Bua na Hamshakin Mai Arziki na 4 a Afrika, Dangote na ta Tafka Asara. Hoto daga NGX
Asali: Facebook

Haka zalika, kafar dake Amurka ta ruwaito yadda Rabiu ya zama tilo cikin jerin biloniyoyin Afirka 10 da ya samu kumbatsar dukiyarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tumbatsar arizikinsa na da nasaba da irin namijin kokarin da kadarorin kasuwancin sa suka yi a Najeriya da wadanda suka hada; kamfanin siminti, matatar sukari da kasuwancin gidaje.

Wannan haurawar da yayi da kamfanonin suka samu a kasuwanci ne ya karfafa matsayinsa a Najeriya a matsayin mutum na biyu da yafi kowa kudi a kasar, gami da rufe tazarar dake tsakaninsa da mutumin da yafi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote.

Kimar arzikinsu a watan Janairu 2022

1. Aliko Dangote - $13.9 biliyan.

2. Johann Rupert da iyalansa - $11 biliyan.

3. Nicky Oppenheimer da iyalansa - $8.7 biliyan.

4. Nassef Sawiris - $8.6 biliyan.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Najeriya Suka Share Hawayen Wata Dattijuwa Da Ke Kwana a Titi, An Sama Mata Muhalli

5. Abdulsamad Rabiu - $7 biliyan.

6. Mike Adenuga - $6.7 biliyan.

7. Issad Rebrab da iyalansa - $5.1 biliyan.

8. Naguib Sawiris - $3.4 biliyan.

9. Patrice Motsepe - $3.1 biliyan.

10. Koos Bekker - $2.7 biliyan.

Kimar arzikinsu a Disamba, 2022 :

1.Aliko Dangote - $12.9 biliyan.

2.Johann Rupert da iyalansa - $ 9.6 biliyan.

3.Nicky Oppenheimer da iyalansa - $8.6 biliyan.

4.Abdulsamad Rabiu - $8.1 biliyan.

5.Nassef Sawiris - $7 biliyan.

6.Mike Adenuga - $5.8 biliyan.

7.Issad Rebrab da iyalansa - $ 5.1biliyan.

8.Naguib Sawiris - $3.4 biliyan.

9. Patrice Motsepe - $2.7 biliyan.

10.Koos Bekker - $2.5 biliyan.

Dangote ya samu karuwar N2.49trn

A wani labari na daban, hamshakin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya samu N2.49 tiriliyan a cikin sa'a 24.

Asali: Legit.ng

Online view pixel