Kwankwaso Ya Zauna da Jagororin APC da PDP a Kaduna, Ya Shigar da su NNPP

Kwankwaso Ya Zauna da Jagororin APC da PDP a Kaduna, Ya Shigar da su NNPP

  • A lokacin da siyasa take daukar zafi a Najeriya, jam’iyyar NNPP ta samu karin ‘yan siyasa a jihar Kaduna
  • Wasu ‘yan siyasar karamar hukumar Kaduna ta Arewa sun hadu da Rabiu Kwankwaso, sun shiga NNPP
  • Irinsu Hon. Shehu ABG, Muhammad Sunusi Liman, Haruna Isah Mami da magoya bayansu sun sauya-sheka

Abuja - A yammacin Talata, 6 ga watan Disamba 2022, wasu daga cikin Kansiloli masu-ci a jihar Kaduna suka kai wa Rabiu Musa Kwankwaso ziyara.

Kamar yadda ya yi bayani a shafinsa¸ Rabiu Musa Kwankwaso yace ya gana da Kansilolin karamar hukumar Kaduna ta Arewa a gidansa a birnin Abuja.

Kansilolin a karkashin jagorancin Rt Hon Haruna Inuwa Mabo sun ayyana kansu a matsayin ‘ya ‘yan jam’iyyar adawa ta NNPP da suka kai masa ziyara.

Hon. Haruna Mabo ya taba rike shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo Ya Nuna Inda Ya Dosa, Bai Goyon Bayan Atiku da Kwankwaso

Hon. Mabo ya jagoranci 'yan siyasa zuwa NNPP

Sauran ‘yan tawagar da aka karba a NNPP sun hada da Hon. Aminu Ayuba Jibril, Hon. Salisu Umar, Hon. Haruna Isah Mami da Hon Muhammad Liman.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yan siyasar da suka fice daga jam’iyyunsu zuwa NNPP sun fito ne daga mazabun Kawo, Liman, Unguwar Dosa da kuma Shaba a yankin Kaduna ta Arewa.

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da sababbin shiga NNPP Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Hon. Shehu ABG sun bar PDP

Har ila yau, babban jagoran na NNPP na kasa yace jam’iyyarsu ta karu da Hon Bashir Isah daga mazabar Unguwar Shanu da kuma irinsu Hon. Shehu ABG.

Hon. ABG ya taba zama ‘dan majalisar wakilan tarayya amma ya rasa kujerarsa a 2015. Daga baya ya nemi tikitin jam’iyyar PDP a 2023, amma ya rasa.

Tsohon mai ba Gwamnan Kaduna shawara a kan harkokin da suka shafi matasa, Hon Aliyu A. Abdulrahman Haruna yana cikin sababbin shiga NNPP.

Kara karanta wannan

Mafi Yawan Yara A Arewa Na Fama Da Talaucin Kayau, Wani Bincike Ya Nuna

A jawabin da ya fitar a Twitter, ‘dan takarar shugaban kasar ya yi masu maraba da shigowa jam’iyya mai kayan dadi, yana sa ran za su kai labari a zabe.

Masu hasashen siyasa suna gani jam’iyyar NNPP za ta iya kawo cikas ga APC mai mulki da musamman PDP a 2023 a jihar ta Kaduna da makwabtanta.

Ina da kudi - Asiwaju Bola Tinubu

Kamar yadda labari ya zo a makon nan, Bola Tinubu ya amsa tambayoyi a kan zargin da ake yi masa na satar kudi da kuma taba baitul-malin jihar Legas.

‘Dan takarar shugaban kasar yace babu hujjar da ke nuna ya ci kudin gwamnati, yace a dalilin hannun jari da gadon gidaje da ya samu ne ya zama Attajiri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel