Hawaye Yayin da Wani Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Kwanta Dama a Oyo

Hawaye Yayin da Wani Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Kwanta Dama a Oyo

  • Jam'iyyar PDP ta rasa ɗaya daga cikin manyan fitattun mambobinta a jihar Oyo, Olugbade Ojelabi, Allah ya masa rasuwa
  • A wata sanarwa da kakakin majalisar dokokin jihar ya fitar yace Marigayin ya cika ne ranar Litinin 5 ga watan Disamba, 2022
  • Har zuwa numfashinsa na karshe yana da shekaru 59, Mamacin ya kasance shugaban PDP a shiryyar Oyo ta kudu

Oyo - Olugbade Ojelabi, shugaban jam'iyyar PDP a shiyyar sanatan Oyo ta kudu, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 59 a duniya.

New Telegraph ta tattaro cewa Jigon PDP ya ce ga garinku ne da safiyar ranar Litinin 5 ga watan Disamba, 2022.

Kakakin majalisar Oyo da Jigon PDP.
Hawaye Yayin da Wani Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Kwanta Dama a Oyo Hoto: Hon. Adebo
Asali: Facebook

Kakakin majalisar dokokin Oyo ya tabbatar da mutuwar

Kakakin majalisar dokokin jihar, Adebo Ogundoyin, ya tabbatar da rasuwar jigon a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace labarin rasuwar ɗan siyasan abun bakin ciki ne da takaici kuma babban rashi ne ga al'ummar garin Eruwa.

"Labarin ya jefa ni cikin kaɗuwa, babban rashi ne ga mutanen garin Eruwa, Ibrapaland da jam'iyyar mu a Oyo. Na rasa bakin magana domin abun kamar mafarki, ya halarci taron masu ruwa da tsaki da muka yi jiya a Eruwa."
"Kuma bai nuna alamun rashin lafiya ba ko kaɗan, ya ba da gudummuwa a taron yadda ya saba. Rasuwarsa abun mamaki ce ba kaɗan ba, na rasa ɗan garin mu domin mun fito ne daga gunduma ta 2 a Anko, Eruwa."
"Na ɗauke shi uba, jagora kuma abun koyi mai bamu kwarin guiwa, basirarsa a siyasa ta zarce a take ta, abun da ɗaci."

- odebo Ogundoyin.

Wasu 'yan Najeriya sun jajanta rasuwar mutumin

Fatal Jimoh yace:

"Mun yi rashin jigon siyasa, makarantarmu ɗaya. Dukkan mu daga Allah muke kuma gare shi zamu koma, Allah ya sa ransa cikin salama."

Abolanle Stephen yace:

"Mutuwar bazata mai zafi da kaɗuwa, marigayin ya halarci wani ɗaura aure ranar Asabar. Ya Allah wa zamu tuhuma? Muna fatan ran ɗan uwanmu ya samu salama a wurin mahaliccinsa."

Allah Ya Yiwa Sakataren PDP A Jihar Bauchi Rasuwa

A wani labarin kuma Sakataren jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Bauchi, Sani Muhammed Chinade, ya rigamu gidan gaskiya

Mai magana da yawun PDP na jihar, Yayanuwa Zainabari, wanda ya tabbatar da lamarin yace sakataren ya rasu ne ranar Asabar da ta gabata bayan yar rashin lafiya.

Bayanai sun nuna cewa Ƙauran Bauchi ya jagorancin tawagar shugabannin PDP da masu faɗa aji zuwa garin Chinade don yi wa iyalansa da al'umma ta'aziyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel