Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yiwa Sakataren PDP A Jihar Bauchi Rasuwa

Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yiwa Sakataren PDP A Jihar Bauchi Rasuwa

  • Allah ya yiwa sakataren jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, Sani Mohammed Chinade, rasuwa a daren ranar Asabar
  • Kakakin jam'iyyar PDP a jihar, Yayanuwa Zainabari, ne ya sanar da labarin mutuwar a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba
  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya jagoranci tawagar PDP da jami'an gwamnati don yiwa iyalansa ta'aziyya

Bauchi - Labarin da muke samu daga jaridar Nigerian Tribune shine cewa sakataren jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Bauchi, Sani Muhammad Chinade, ya rasu.

Sakataren labarai na PDP, Yayanuwa Zainabari ne ya tabbatar da labarin mutuwarsa a wata hira da aka yi da shi ta wayar taro a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba.

Logon PDP da gwamnan Bauchi
Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yiwa Sakataren PDP A Jihar Bauchi Rasuwa Hoto: Bauchi State
Asali: Twitter

Ya yi fama da rashin lafiya

Zainabari ya bayyana cewa marigayin ya kwanta dama ne a daren ranar Asabar, 3 ga watan Disamba bayan yar gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Lugude da Gurfana a Kotu, Dalibin da ya Zolaya Aisha Buhari ya Koma Makaranta

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A halin da ake ciki, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ya jagoranci sauran shugabannin PDP da manyan jami’an gwamnati zuwa Chinade, karamar hukumar Katagun domin yiwa yan uwa da mutanen kauyen ta’aziyar rashin da suka yi.

Rawar ganin da marigayin ya taka a PDP

Bala Mohammed ya bayyana mutuwar Sani Chinade a matsayin babban rashi ga PDP a jihar Bauchi da kasar baki daya yana mai cewa marigayin ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar a matsayinsa na tsohon ma’aikacin gwamnati kafin ya zama sakataren PDP.

Gwamnan ya kara da cewar a matsayinsa na sakataren PDP tsawon shekaru shida da suka gabata, marigayi Sani Chinade ya bayar da gagarumin gudunmawa wajen nasarar jam’iyyar a zaben 2019.

Da yake addu’an Allah ya ji kansa, gwamnan ya bukaci yan uwanda da su amshi hakan a matsayin hukuncin Allah domin duk mai rai sai ya dandani dacin mutuwa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Uwargidan Shugaban Kasa ta Huce, Ta Janye Karar Dalibin da ya ‘Zageta’

Yan sanda sun cika hannu da wasu masoya da suka halaka jinjiri sabon haihuwa

A wani labari na daban, rundunar yan sandan jihar Jigawa ta ce jami'anta sun cika hannu da wata mata da saurayinta kan binne jinjirinsu sabon haihuwa da suka yi.

Ahmadu Sale dai ya dirkawa Balaraba Shehu ciki ba tare da aure ba inda ita kuma ta tona rai ta binne jinjinrin da cikin ya haifar jim kadan bayan isowarsa duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel