Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Dawo da ‘Yan Takarar PDP na Jihar Ogun

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Dawo da ‘Yan Takarar PDP na Jihar Ogun

  • Kotun daukaka kara dake jihar Ogun tayi fatali da hukuncin wata babbar kotun tarayya da ta kori dukkan ‘yan takarar PDP na jihar
  • A hukuncin kotun kasan, tayi umarni ga shugabannin jam’iyyar na jihar da su hanzarta dake zaben fidda gwani a cikin kwanaki 14
  • Sai dai Mai shari’a Folasade Ojo tace hukuncin kuskure ne saboda kwamitin ayyukan na kasa na PDP ne kadai ke da karfin ikon zaben fidda gwani

Ogun- Kotun daukaka kara tayi fatali da hukuncin wata babbar kotun tarayya dake Abeokuta ta jihar Ogun wacce tayi umarnin a sake zabukan fidda gwanin jam’iyyar PDP a jihar.

Kotun daukaka kara
Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Dawo da ‘Yan Takarar PDP na Jihar Ogun. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kotun daukaka karar dake Ibadana ya bada wannan umarnin a hukuncin da ya yanke a ranar Litinin.

Premium Times ta rahoto cewa, mai shari’a O O Oguntoyinna babbar kotun a ranar 27 ga watan Satumba ya umarci kwamitin zababbun shugabannin PDP na jihar da su yi sabon zaben fidda gwani cikin kwanaki 14.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma yayin yanke hukuncin daukaka karar da PDP tayi, Mai shari’a Folasade Oko ta kotun dauakaka karar tare hukuncin kotun kasan kuskure ne saboda kwamitin ayyuka na kasa na PDP ne kadai suke da ikon yin zaben fidda gwani.

Jam’iyyar PDP a jihar Ogun ta rabe uku inda take da ‘yan takara uku a kowanne tsagi kuma suke ikirarin kasancewa ‘yan takarar Gwamna jihar.

Sai dai hedkwatar jam’iyyar dake Abuja Ladi Adebutu kadai take kallo matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar.

Abinda ya faru a jihar

Tsagi biyu na jam’iyyar PDP don sun yi zabukan fidda gwani wanda ya samar da Oladipupo Adebutu da Segun Sowunmi matsayin ‘yan takarar gwamnan jihar a zaben 2023 mai zuwa.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, zaben fidda gwanin da ya samar da Sowunmi an gano cewa jami’an IPAC ne suka lura dashi.

Sai dai wanda ya samar da Adebutu, tsohon ‘dan majalisar jihar ne shugabannin jam’iyyar suka ce basu san da shi ba.

Jimi Lawal, wani ‘dan takarar kujerar Gwamnan jihar ne ya maka kara gaban wata kotun tarayya kan jerin sunayen deliget din da tsagin Sikirulahi Ogundele suka yi amfani da shi wanda ya samar da Adebutu matsayin ‘dan takara.

Sauran ‘yan takarar sun kalulanci ingancin shugabancin tsagin Sikirulahi Ogundele.

A karkashin shugabancin Oguntoyinbo, kotun ta soke zabukan fidda gwanin da aka yi a jihar inda ta bukaci a sake sabon zabe.

A yayin yanke hukunci kan daukaka kara da PDP tayi, kotun daukaka karar ya soke hukuncin babbar kotun tarayyan.

Kotun daukaka kara ta jaddada ingancin takarar Machina

A wani labari na daban, kotun daukaka kara dake zama a Abuja tace Bashir Machina ne halastaccen ‘dan takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa.

Kotun ta jaddada hukuncin kotun kasa da ita wacce tace zaben fidda gwanin 28 ga Mayu ne INEC ta lura dashi kuma shi ne sahihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel