Kotun Daukaka Kara: Machina Ya Sake Lallasa Lawan, Kotu Ta Tabbatar da Shi Matsayin ‘dan Takara

Kotun Daukaka Kara: Machina Ya Sake Lallasa Lawan, Kotu Ta Tabbatar da Shi Matsayin ‘dan Takara

  • Bashir Sheriff Machina, ‘dan takarar kujerar sanatan Yobe ta Arewa, ya sake lallasa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a kotun daukaka kara
  • A hukuncin kotun na wannan karon, ta bukaci jam’iyyar APC da ta daukaka kara da ta biya Machina makuden kudi har Naira miliyan daya
  • Kotun tace zaben fidda gwanin da aka yi ranar 28 ga Mayu, wanda ya samar da Machina matsayin ‘dan takara, shi ne sahihi ba wanda ya samar da Lawan ba

FCT, Abuja - Wata kotun daukaka kara dake zama a Abuja ya jaddada cewa Bashir Sheriff Machina ne sahihin ‘dan takarar jam’iyyar na kujerar sanatan Yobe ta arewa a jihar Yobe.

Bashir Machina
Kotun Daukaka Kara: Machina Ya Sake Lallasa Lawan, Kotu Ta Tabbatar da Shi Matsayin ‘dan Takara. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Kotun daukaka karar ta jaddada hukuncin wata babbar kotun tarayya dake zama a Damaturu dake jihar Yobe wacce tace shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ba shi ne ‘dan takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa ba a zaben shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Tayi Fatali da Hukuncin Kotun Tarayya kan ‘Yan takarar PDP a Ogun

Kotun ta ce Lawan bai yi zaben fidda gwanin da jam’iyyar APC tayi ba na ranar 28 ga watan Mayun 2022, Channels TV ta rahoto.

A yayin yanke hukunci kan daukaka karar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, yayi, kwamitin alkalai uku da suka samu jagorancin Monica Dongban-Mensem, sun yanke hukuncin cewa zaben fidda gwanin da jam’iyyar APC tayi a ranar 9 ga watan Yuni ba sahihi bane saboda yayi karantsaye ga kundin tsarin mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dokar ta bukaci shigar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a yayin zaben fidda gwanin wanda zaben ranar 9 ga watan Yuni an yi shi ne ba tare da INEC ta lura da shi ba.

Jam’iyyar APC da kanta ta daukaka kara kuma tafi son Lawan matsayin ‘dan takarar amma sai bata sa shi matsayin mai daukaka kara ta biyu ba.

Kara karanta wannan

Aisha Binani Ta Koma Mahaifarta Bayan Nasarar Da Ta Samu a Kotu, Ta Samu Kyakkyawar Tarba Daga Masoya

Lawan ya bayyana a matsayin wanda ake kara na biyu, lamarin da ya nuna shi da APC ba a bangare daya suke ba yayin da suke neman cimma burin, jaridar Vanguard ta rahoto.

Daukaka karar bata da amfani ko kadan saboda dukkanta akwai gazawa cikinta.

Mai daukaka kara, APC zata biya Bashir Shettima kudi har N1 miliyan.

Kotu ta fattakai Lawan, ta tabbatar da Shettima ‘Dan takara

A wani labari na daban, kotun daukaka kara ta ayyana Bashir Machina matsayin ingantaccen ‘dan takarar Sanatan Yobe ta arewa.

Kotun tace Lawan bai yi zaben fidda gwanin 28 ga Mayu ba wand INEC ta lura dashi a Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel