‘Dan Takarar Shugabancin Kasa na PDP Zasu Gana da Kungiyar CAN

‘Dan Takarar Shugabancin Kasa na PDP Zasu Gana da Kungiyar CAN

  • Atiku Abubakar, ‘dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP, ya je ganawa da shugabannin Kungiyar Kiristoci ta kasa
  • Kungiyar Kiristoci ta kasa ta fara tattaunawa da ‘yan takarar shugabancin kasan inda suke gabatar musu da bukatunsu
  • Atiku ya samu rakiyar Gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP na kasa

Abuja - ‘Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Talata ya isa hedkwatar kungiyar Kiristoci ta Najeriya domin zantawa da shugabanninsu.

Atiku, Okowa da CAN
‘Dan Takarar Shugabancin Kasa na PDP Zasu Gana da Kungiyar CAN. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa, CAN ta fara zantawa da ‘yan takarar shugabancin kasan inda suke gabatar musu da bukatu.

Atiku ya isa hedkwatar CAN din tare da mataimakinsa na takara, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Wike da Sauran Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Sam Ba Zasu Taya Atiku Kamfen Ba

Sauran dake cikin tawagar sun hada da Gwamna na jihar Taraba, Darius Ishaku, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Namadi Sambo, Cif Tom Ikimi, shugaban Emeritus na Daar Communications Plc, Raymond Dokpesi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da: tsohon gwamna Cross River, Liyel Imoke, Sanata Philip Aduda, Sanata Dino Melaye, Timi Alaibe, Kenneth Imasuagbon, Dele Momodu, Boni Haruna da sauran shugabannin jam’iyyar suna daga cikin tawagar.

Karin bayani na nan tafe…

Asali: Legit.ng

Online view pixel