Gwamna Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Ce Zai Taimakawa Peter Obi a Gangamin Zaben 2023

Gwamna Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Ce Zai Taimakawa Peter Obi a Gangamin Zaben 2023

  • Gwamna Wike ya ce zai taimakawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi da abin da yake bukata na kamfen a jihar Ribas
  • Wike ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Obi a jiharsa a bikin kaddamar da wasu ayyukan da ya yi
  • Jam'iyyar PDP na cikin rabuwar kai tun bayan da Wike da wasu gwamnoni hudu suka fara neman tsige shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu

Jihar Ribas - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana aniyarsa ta taimakawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da kayayyaki da ba a rasa ba a gangamin neman zabensa, Channels Tv ta ruwaito.

Wike ya kuma bayyana cewa, tsohon gwamnan na Anambra, Obi na da abin da ake bukata don mulkar Najeriya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiharsa yayin da Obi ya zo don kaddamar da wata gadar sama ta Nkpolu-Oroworokwo a Fatakwal.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Rikici da Atiku, Wike Zai ba Peter Obi Gudumuwar Lashe Zabe a 2023

Peter Obi zai samu tallafin kamfen daga gwamnan PDP Wike
Gwamna Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Ce Zai Taimakawa Peter Obi a Gangamin Zaben 2023 | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar Wike ga Peter Obi:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duk lokacin da kake son yin kamfen a jihar nan, ka sanar da ni, duk tallafin shirye-shirye, za mu samar muku."

Peter Obi ya kai ziyara jihar Ribas don kaddamar da wani aiki

Obi da abokin takararsa, Datta Baba-Ahmad sun dura jihar Ribas domin kaddamar da gadar sama ta 9 da gwamnan ya gida.

Sun samu tarba mai kyau daga jama'a da dama, ciki har da 'yan a mutun Obi da aka fi sani da 'Obidients'.

Idan baku manta ba, gwamna Wike da wasu gwamnonin PDP hudu sun sanya jam'iyyar cikin damuwa tun bayan da suka fara nuna adawa da shugabancin jam'iyyar.

Wike ya ci gaba da rabar 'yan jam'iyyar adawa, inda ya gayyaci Tinubu da Peter Obi zuwa jiharsa don kaddamar da ayyukan da ya yi, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Na Maka Magiya Dan Allah' Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Roki Wike Ya Goya Masa Baya a 2023

A wurin kaddamar da aikin, Wike ya tuna da irin kalubalen da Obi ya fuskanta a PDP, inda yace ba zai bar jam'iyyar a hannun 'yan fashi ba.

CAN ta gayyaci 'yan takarar shugaban kasa don tattaunawa dasu

A wani labarin na daban, kungiyar kiristocin Najeriya ta bayyana gayyatara 'yan takarar shugaban kasa domin tattauna muradan kiristocin kasar nan.

An gayyaci Peter, Atiku da sauran 'yan takara, inda kungiyar za ta fadi abin da take bukata a yiwa mambobin bayan zaben 2023.

Jam'iyyun siyasa na ci gaba da tallata 'yan takara gabanin zaben 2023, lamura na kara tafiya a gangamin kamfen a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel