Yadda ‘Dan Majalisar Legas Ya Rasu Wajen Taron Kamfen Bola Tinubu a Garin Jos

Yadda ‘Dan Majalisar Legas Ya Rasu Wajen Taron Kamfen Bola Tinubu a Garin Jos

  • An samu karin bayani a game da silar mutuwar Sobur Olawale a wajen taron yakin zaben Jam’iyyar APC
  • ‘Dan majalisar ya gamu da ajalinsa ne a yayin da dinbin mutane suka danne shi a filin kamfe a jihar Filato
  • Mutuwar Hon. Sobur Olawale ta girgiza ‘yan siyasa musamman ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen Legas

Jos - Sababbin bayanai sun bayyana a game da mutuwar ‘dan majalisar Mushin II a majalisar dokokin jihar Legas, Hon. Sobur Olawale.

Jaridar Vanguard ta tattauna da wani wanda ya san yadda Sobur Olawale wanda aka fi sani da Omititi ya cika a taron yakin zabe na APC.

Wani wanda abin ya faru a gaban idonsa ya zanta da jaridar ba tare da ya bari an ambaci sunansa ba, ya bayyana cewa sun dangana.

Kara karanta wannan

Jagora a Jam’iyyar LP Ya Dawo APC, Yace Peter Obi Ba Za Su Kai Labari a 2023 ba

A cewar majiyar, dandazon mutane suka dura kan Honarabul Olawale a filin wasan da aka bude takarar Bola Tinubu/Kashim Shettima.

“Olawale bai yi sa’a ba, yana kokarin neman hanya a cikin dandazon jama’a, sai suka danne shi a wajen taron bude yakin neman zaben APC.
Amma mun rungumi kaddarar Ubangiji."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Majiya

Taron Kamfen Bola Tinubu a Garin Jos
Taron kamfen APC a Jos Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Ganin karshe na Omititi

Rahoton yace ganin da aka yi wa ‘dan majalisar na Mushin na karshe shi ne a wajen wani wasan kwallon kafa da aka shirya a makon da ya wuce.

An shirya kwallon kafan ne domin taya Mudashiru Obasa murnar cika shekaru 50 a Duniya. Rt. Hon. Obasa shi ne shugaban majalisar dokokin Legas.

Kamar yadda muka samu labari, Omititi ya zama mai tsaron raga a wasan kwallon da aka yi. Ashe saura ‘yan kwanaki suka rage masa a lokacin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ‘Dan Majalisa Ya Fadi Ana Tsaka da Ralin Tinubu, Ya Rasa Ransa

An yi babban rashi a Legas

Kafin rasuwarsa, shi ne shugaban kwamitin harkokin kananan hukumomi da alaka da al’umma, ‘dan siyasar yana kan wa’adinsa na biyu a majalisa.

Kafin wannan lamarin ya auku, Omititi yana gagarumin shirye-shiryen auren da diyarsa. An sa rana za ayi auren ne nan da makonni biyu a Legas.

PDP za ta ci Legas inji Ayu

Dazu aka ji labari shugaban jam’iyyar PDP ya karbi aikin da kwamitin Eyitayo Jegede ya yi. ‘Dan siyasar aka ba nauyin sasanta rikicin Legas da Osun

Jigon jam'iyyar kuma tsohon ‘dan takaran PDP a zaben gwamnan jihar Ondo, Jegede yace a sanadiyyar aikinsu ne jam'iyyar ta ci zabe a jihar Osun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel