Ana Wata Ga Wata: Kotu Ta Sake Soke Zaben Dan Takarar Gwamna Na APC a Taraba

Ana Wata Ga Wata: Kotu Ta Sake Soke Zaben Dan Takarar Gwamna Na APC a Taraba

  • A karo na biyu, babbar kotun tarayya ta sake soke zaben fidda dan takarar gwamna na APC a jihar Taraba
  • Kotun ta sake tsige Sanata Emmanuel Bwacha daga matsayin dan takarar gwamna na APC a jihar ta arewa
  • Yayin da tayi umurnin sake sabon zabe cikin kwanaki 14, kotun ta kuma umurci Bwacha da ya daina daukar kansa a matsayin dan takarar APC a jihar

Taraba - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta soke zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Taraba da ya samar da sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takara.

Da farko wata babbar kotun tarayya da ke Jalingo, babban birnin jihar ta fatattake shi daga matsayin wanda ke rike da tutar takarar gwamna na jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Gasar 2023: Za a Yi Gasar Karatun Al-Qur'ani Na Kasa, An Fadi Jihar Da Za Ta Karbi Bakuncin Taron

Kotu ta yi umurnin sake sabon zabe cikin kwanaki 14

Yayin zaman kotu na ranar Talata, 15 ga watan Nuwamba, Justis Obiora Egwuatu ya yi kira ga APC da ta sake sabon zaben fidda dan takarar gwamna a jihar cikin kwanaki 14, jaridar Leadership ta rahoto.

Emmanuel Bwacha
Kotu Ta Sake Soke Zaɓen Dan Takarar Gwamna Na APC a Wata Jihar Arewa Hoto: Emmanuel Bwacha
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta kuma umurci Bwacha da ya daina daukar kansa a matsayin dan takarar gwamna na APC a jihar, rahoton Premium Times.

Hukuncin kotun ya biyo bayan wata kara da sanata mai wakiltan Taraba ta tsakiya, Yusuf A. Yusuf ya shigar.

Da yake jayayyar cewa ba a gudanar da zaben fidda dan takarar gwamnan a jihar Taraba ba, Yusuf ya tambayi dalilin da yasa APC a matakin kasa ta ayyana Bwacha a matsayin wanda yayi nasara.

Shugabancin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta maka sanatan a kotu jim kadan bayan sauya shekarsa zuwa APC.

Kara karanta wannan

Mu Na Nan Kan Matsayar Da Uwar Kungiyar Kiristoci CAN Ta Dauka Na Kin Goyan Bayan Tunubu

Yayin da Bwacha ya daukaka kara kan hukuncin kotun Jalingo, zuwa yanzu ba a sani ba ko zai sake daukaka kara a kan hukuncin na yau wanda ya gudana a Abuja.

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam’iyyar Labour Party ta yi babban kamu a jihar Taraba bayan wasu hadiman Gwamna Darius Ishaku biyu sun sauya sheka daga PDP zuwa cikinta.

Hadiman gwamnan da suka hada Mbatudi Agabi da Shekarau Masaibi sun ce hakan zai basu damar goyon bayan dan takarar da suke muradi a babban zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel