Jihar Zamfara Za Ta Dauki Nauyin Gasar Karatun Al-Qur’ani Ta Kasa

Jihar Zamfara Za Ta Dauki Nauyin Gasar Karatun Al-Qur’ani Ta Kasa

  • Jihar Zamfara ce mai masaukin baki yayin da za a gudanar da gasar karatun Al-Qur’ani na bana a watan gobe
  • Gwamnatin Bello Matawalle ta ba da tabbacin ci gaba da tallafawa gasar karatun Qur’ani ta bangaren kudi don ganin an yi shi cikin nasara
  • An kuma bukaci al’ummar jihar da su zamo masu nuna karamci ga mahalarta taron a matsayinsu na masu masaukin baki

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala shirye-shirye don daukar nauyin gasar al-Qur’ani ta kasa wanda za a yi a ranar 16 ga watan Disamba.

Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a wajen bikin bude gasar al-Qur’ani na jihar wanda aka yi a Gusau a jiya Talata, jaridar The Nation ta rahoto.

Matawalle
Jihar Zamfara Za Ta Dauki Nauyin Gasar Karatun Al-Kur’ani Ta Kasa Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Gwamnatin Zamfara za ta taimaka da kudi don gudanar da gasar

Kara karanta wannan

Sanata Binani vs Nuhu Ribadu : Kotu Daukaka Ta shirya yanke hukunci kan zaben fidda gwanin jihar Adamawa

Nasiha ya bayar da tabbacin cewa a shirye gwamnatin jihar take ta bayar da duk gudunmawar da ake bukata na kudi don gudanar gasar cikin nasara da ba baki masu halartan gasar kulawar da yakamata, Radio Nigeria Kaduna ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“A matsayinta na jihar shariya, gwamnatinmu tana bayar da muhimmanci ga bangaren shari’a da kuma samar da duk abubuwan bukata don gudanar da gasar karatun Qur’ani na jiha da kasa baki daya cikin nasara a jihar."

Da yake jawabi a taron, babban bako Dr. Atiku Balarabe, ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi koyi da koyarwar shari’a ta hanyar bayar da cikakken kulawa gab akin da za su zo jihar.

Balarabe ya ce dole mu yi biyayya ga koyarwar Qur’ani a matsayinta na littafi mafi daraja don cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyoyi Sun Yi Gangami a Wata Jihar Arewa, Sun Yi Alkawarin Kawowa Tinubu Kuri'u Miliyan 4

Ka'idojin shiga gasar

A cewar sakataren kwamitin gasar karatun Qur’ani a jihar, Malam Sadiqu Sadiq, ya ce gasar karatun na jihar karo na 26 zai samu mutane 367 daga fadin kananan hukumomi 14 na jihar.

Ya kara da cewar ka’idojin gasar wanda ke dauke da nau’I bakwai shine cewa dole wadanda zasu shiga hasar su haura shekaru 25, dole su wakilci mahaifarsu, kuma dole su iya kawo cikakkiyar hadda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel