Rigimar PDP: Gwamnan Bauchi Ya Fadi Abun Da Ya Haɗa Shi Da Gwamnonin G5

Rigimar PDP: Gwamnan Bauchi Ya Fadi Abun Da Ya Haɗa Shi Da Gwamnonin G5

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya nuna jin daɗinsa bisa ziyarar gwamnonin G5 karkashin Wike
  • Yace kamata ya yi ace suna tare a inuwa ɗaya amma ba su neme shi ba saboda wani dalili da suka barwa kansu sani
  • Gwamnan ya nuna fushinsa kan yadda aka ware shi a tafiyar PDP, tuni Atiku ya fara kokarin shawo kansa

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, yace akwai wani abu da ya haɗasu inuwa ɗaya da gwamnonin tawagar G5 karkashin jagorancin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Tawagar G5 ta ƙunshi Wike, Samuel Ortom na jihar Benuwai, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ipeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, dukkansu basu ga maciji da ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Gwamna Wike da Bala Muhammed.
Rigimar PDP: Gwamnan Bauchi Ya Fadi Abun Da Ya Haɗa Shi Da Gwamnonin G5 Hoto: Nyesom Wike, Senator Bala Muhammed
Asali: Facebook

Daily Trust tace Atiku ya yi kokarin rarrashin gwamnan Bauchi amma a ranar Laraba aka hangi Wike ya jagoranci tawagarsa sun kaiwa gwamna Muhammed ziyara.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Abin Da Yasa Ni, Ortom Da Wasu Muka Ziyarci Gwamnan Bauchi", Wike

Gwaman Muhammed ya bayyana cewa ya ji daɗin ziyarar da gwamnonin suka kai masa har jiharsa ta Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa yace:

"Gwamnonin G5 kamar yadda suka raɗa wa kansu suna sun kira kansu da 'Tawagar gaskiya'. Kamata ya yi ace ina tare da su amma basu neme ni ba saboda wani dalili da su kaɗai suka sani."
"Amma ina da alaƙa mai ƙarfi da su, kowane ɗaya daga cikinsu, babu ranar da zata zo ta wuce bamu yi waya da kowanensu ba saboda a siyasa kana tafiya ne da mutanen da kuke da ra'ayi iri ɗaya."
"Muna da wani ra'ayi da yazo ɗaya, sun san cewa na tsani cin amanar jam'iyya, siyasa ta kunshi yaudara da zagon ƙasa amma da ka tuna akwai masu goya maka baya sai kaji kamar ka cimma gaci."

Tun farko, gwamna Wike yace sun kai wannan ziyara ne domin nuna wa abokinsu, gwamnan Bauchi cewa ana tare kuma sun san cewa yana neman tazarce.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Daga Cikin Gwamnonin Tsagin Wike Na Shirin Yaudararsa, Zasu Koma Bayan Atiku

Babu wanda ga kaiwa Ayarin Atiku hari a Borno - APC

A wani labarin kuma jam'iyyar PDP ya musanta ikirarin kakakin kamfen PDP cewa wasu baragurbi sun farmaki Ayarin Atiku a Maiduguri

A wata sanarwa da shugaban APC reshen jihar Borno ya fitar, yace bai ji daɗin ƙaryar da Dino Melaye ya yi ba kan lamarin.

A cewarsa, tun zuwan gwamna Babagana Zulum, ya haramta duk wani harkar dabanci a jihar kuma APC jam'iyya ce mai bin doka sau da ƙafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel